✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dan Majalisar Wakilai Haruna Maitala ya rasu

Ya yi hatsari a hanyarsa ta zuwa Jos daga Abuja

Allah Ya yi wa Dan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazabar Jos ta Arewa da Bassa da ke Jihar Filato, Alhaji Haruna Maitala Jingir rasuwa, a wani mummunan hatsarin mota ranar Juma’a da dare.

Hatsarin ya faru ne a lokacin da marigayin ya taso daga Abuja, zai zo garin Jos a motarsa.

Wata majiya daga iyalan marigayin ta tabbatar wa Aminiya cewa marigayin ya rasu ne a wani asibiti da ke garin Kwoi, a Karamar Jama’a, Jihar Kaduna.

Majiyar ta ce hatsari ya kuma yi sanadin rasuwar dan marigayin mai suna Jafaru Haruna da direban motar.