✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

dan majalisar tarayya ya tallafa wa al’ummar Rofiya da masaukin baki

Daga Umar  M. Gombe Canjin da al’ummar kasar nan suka yi na shugabancin kasar nan abin a yaba ne, wanda hakan ya sa aka samu…

Daga Umar  M. Gombe

Canjin da al’ummar kasar nan suka yi na shugabancin kasar nan abin a yaba ne, wanda hakan ya sa aka samu canje-canje a salon siyasar kasar nan. Shugaban karamar hukumar Agwara ta jihar Neja, Hon. Jafaru Muhammad Agwara ne ya bayyana hakan a lokacin karbar tashar mota mai dauke da shaguna da dakin baki da dan majalisar wakilai ta tarayya mai wakiltar Bargu da Agwara, Hon. Umar Muhammad Rofia ya gina a bakin gabar ruwan Rofiya-Zamare ya mika kulawarsa ga ita karamar hukumar.

Shugaban karamar hukumar ya ce al’umma su kara hakuri domin manufa da muradun gwamnatin Muhammadu Buhari da jam’iyyar APC shi ne samar da walwala da gina tubalin da ‘yan kasa za su amfana da shi. Yanzu haka shirye-shirye ya yi nisa wajen hada hannu da gwamnatin jiha da hukumar RAM da shi dan majalisarmu ta tarayya wajen gina hanyoyi a wannan karkara da ya kai kilimita 57 tsakanin kauyukan da ke hade da juna dan samun saukin safara da kasuwanci.

Da yake karin haske, dan majalisar wakilan, Hon. Umar Muhammad Rofia, ya ce ya samar da wannan waje ne dan bunkasa harkokin kasuwanci a gabar ruwan Rofia da Zamare domin baiwa baki ‘yan kasuwa damar shigowa cikin wannan karkara na karamar hukumar Agwara tare da samar da dakunan kwanan baki da shaguna dan samarwa ita karamar hukuma hanyoyin samun kudin shiga.

Yanzu haka mun kammala aikin hanyar Ganda zuwa Adahe, kuma mun dauki haramar mai da hankali kan aikin hanyar Adahe zuwa Mago da kuma wadda ta tashi daga Mago zuwa Kasabo, burin shi ne saukakawa jama’armu wajen samun saukin gudanar da hanyoyin harkokin kasuwanci ga kananan ‘yan kasuwa da manoma dan samarwa karamar hukuma kudaden shiga.

dan majalisar ya jawo hankalin matasa da su gaggauta mai da hankali wajen mallakar katin zabe wannan zai ba su damar zabarwa kansu nagartattun wakilai a zabuka masu zuwa.

Da suke amsa tambaoyin manema labaru wasu daga cikin matasan yankin na Agwara sun yabawa dan majalisar akan irin muradunsa na kawo canjin a salon siyasar yankin, musamman inda ya zage damtse wajen kawo abubuwan more rayuwa ga al’ummar da yake wakilta tare da samo gurabun aikin daga gwamnatin tarayya, sai dai matasan sun nemi dan majalisar da ya taimaka masu musamman wajen gyara madatsan ruwa da girajen ruwa da ke harkar fito a yankin wanda suke bangaren jihar Kebbi gwamnatin jihar ta gyara amma gefen su da ke karkashin jihar Neja na bukatar kulawar gaggawa ganin yadda motocin daukar kaya ke samun barazanar faduwa wanda hakan koma baya ne babba.

Shugaban jam’iyyar APC na jihar Neja, wanda ya samu wakilcin ma’ajin jam’iyyar ta jiha, Hon. Audu Ibrahim (Abiola) ya ce jam’iyyarsu ta himmantu gaya wajen ganin alkawurran da ta dauka lokacin yakin neman zabe an cika shi, dan haka jam’iyyar ta bada tabbacin kafin cikar wa’adin wannan gwamnatin jama’a za su dara akan abinda suke nema. Taron dai ya samu halartar Uban kasar Agwara, Alhaji Hassan Zakari da Mai Rofia, Malam Muhammadu Isah, da wasu daga cikin jiga-jigan jam’iyyar ta jiha da karamar hukumar Agwara.