Dan majalisar wakilan tarayyar Najeriya mai wakiltar mazabar kananan hukumomin Musawa da Matazu da ke jihar Katsina, Ibrahim Murtala ya fice daga jam’iyyar APC zuwa jam’iyyar adawa ta PDP.
Kakakin majalisar wakilan tarayyar Najeriya Yakubu Dogara ne karanta wasikar ficewar dan majalisar yau a zauren majalisar.
A cikin wasikar dan majalisar ya nuna farin cikinsa na fita daga jam’iyyar APC sakamakon rikicin da ya da baibaye jam’iyyar wanda hakan yasa ya koma PDP.