Dan majilisar dokoki mai wakiltar Karamar Hukumar Birni a Majalisar Dokokin Jihar Kano, Salisu Ahmad Gwangwazo, ya sauya sheka zuwa APC, wanda hakan ya sa ’yan jami’yyar suka karu zuwa 20, PDP kuma ke da 11.
Bayanin hakan ya fito ne a wata wasika da ya aika wa Shugaban Majalisar, Hamisu Chidari kamar yadda mai magana da yawun Kakakin majalisar Malam Uba Abdullahi ya bayyana.
- Hatsari: Mutum 7 sun mutu, wasu 5 sun jikkata a hanyar Legas
- Najeriya za ta tura sojoji 205 samar da tsaro a Gambia
“Ahmad Gwangwazo ya bayyana nuna bangaranci a jagorancin tshouwar jam’iyarsa ta PDP tun daga matakin kasa har zuwa jiha a matsayin dalilinsa na ajiye jam’iyar” a cewar Uba Abdullahi.
” kuma na taya Ahmad Gwangwazo murnar shigowa jam’iyarmu ta APC, kuma muna tabbatar masa cewa jamiyar ba za ta bar shi da sauran magoya bayansa a baya ba a dukkanin sha’aninta” in ji mai magana da yawun Kakakin majalisar.
Ya kuma ce jam’iyarsu na tafiya kan tsarin tafiya da kowa musamman a abubuwan da za su kawo cigaba ga jihar Kano.
“Hakan ne ma ya sa jamiyar APC za ta sake samun nasara a zabukan 2023” in ji shi.