Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Suleja, Tafa da Gurara, Honarabul Lado Suleja, ya raba wa al’ummar mazabarsa tallafin kudi har kimanin naira miliyan hamsin.
Lado Suleja, ya yi rabon kudin ne a ranar Talata ga wasu daga cikin ’yan mazabar da yake wakilta a zauren Majalisar tarayya, inda ya yi alkawarin ci gaba da rabon kudin ga jama’arsa da har zuwa bayan karamar Sallah da mako daya.
- Surutai ba za su sa mu tattauna da ’yan bindiga ba —El-Rufai
- Majalisa ta nemi Buhari ya ayyana dokar ta-baci a Najeriya
Dan Majalisar ya yi rabon kudin ne rukuni-rukuni, inda wadansu suka samu naira miliyan daya yayin da wasu suka samu naira dubu dari biyar-biyar sannan da wadanda aka raba wa naira dubu dari uku da kuma wandanda suka samu naira dubu dari biyu.
Honarabul Lado, ya ce nan gaba kadan akwai kimanin mutane 240 da su ma zai yi musu rabon naira miliyan 100 idan an kammala Azumin watan Ramalana.
Lado, ya bayyana cewa rabon ya zama wajibi a kansa saboda irin gudunmuwa da rawar da suka taka har zuwa matakin samun nasararsa ta zama dan majalisa.
Kazalika, ya bukaci wadanda ya raba wa kudin da su yi amfani da su wurin bunkasa harkokinsu na kasuwanci.