✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dan majalisa ya halarci zaman Majalisa tsirara

Muhawara ta barke bayan da Hon. Amos, ya bayyana babu ko kamfai a jikinsa, a yayin zaman Majalisar.

Wani dan Majalisar Wakilai ya halarci zamanta tsirara, haihuwar uwarsa.

Dan Majalisa William Amos, ya bayyana ne tsirara babu ko kamfai a jikinsa, a yayin da zaman Majalisar ake gudana ta bidiyo a ranar Laraba.

Tun bayan bullar cutar COVID-19 a kasar Kanada, ’yan Majalisar ke halartar zamanta da ta bidiyo maimakon da kansu.

Ana tsaka da zaman na ranar Laraba, kwatsam sai takwarorinsa suka hango shi a tsirara a tsaye tsakanin tutar Kanada da na yankin Quebec  da yake wakilta, sai dai wani abu kamar wayar salula da ke rike hannunsa, ya kare al’aurarsa.

Tun shekarar 2015 Hon. William ke wakilatar Quebec da ke lardin Pontiac na kasar Canada a Majalisar.

Ganin Hon. William a zindir ke da wuya, ’yar majalisa Claude DeBellefeuille daga jam’iyyar adawa ta Bloc Quebecois, ta daga kara tare cewa Dokar Majalisa ta wajabta wa kowane dan Majalisar sanya kwat da ’yar-ciki da laktai da wando a lokacin zamanta.

“Ina takaicin abin da ya faru. Na yi kuskuren kunna bidiyona ne a lokacin da nake canza kaya zan fita motsa jiki. Ina naman afuwar abokan aikina game abin da hakan ya haifar. Ba da gangan da yi ba, kuma hakan ba zai kara faruwa ba,” inji shi.

Mahawara

Da farko Shugaban Majalisar, Anthony Rota, ya musa maganar ta Hon. DeBellefeuille, da cewa shi bai ga abin da take zargi ba, amma daga baya da ya duba ya ce tabbas Hon. William ne a tsirara.

Don haka ya shawarci ’yan majalisar da su rika yin taka-tsantsan a duk lokacin da suke gaban kyamara ko makirfon.

Sai dai kuma ’yan Majalisar da ma’aikata ne kadai suka ga bidiyon Hon. William Amos a tsirara, sauran jama’a ba su gani ba, kasancewa ba shi yake magana ba a lokacin da abin ya faru.

Takwaransa aga jam’yarsa ta Liberal, Mark Holland ya ce Hon. William Amos “ya kadu matuka,” kuma shi ya gamsu da bayaninsa.

“Ba na zaton akwai wata mummunar manufa. Tabbas ba abin da aka so ba ke nan,” inji  Holland.

“Wannan gargadi ne ga kowa, dole ka rika kiyayewa tare da turanin cew kyamararka na kunne a duk sadda za ka yi motsi kuma ka tabbata kana sanye da kaya yadda ya kamata.”