✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dan majalisa na son China ta ceto fasinjojin jirgin kasan Kaduna

Sanatan ya bukaci China ta tallafa wa Najeriya wajen ceto wadanda aka sace yayin harin.

Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa mai kula da harkokin sufurin jirgin kasa, Sanata Abdulfatai Buhari, ya bayyana damuwarsa kan yadda aka kasa ceto wadanda harin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna, ya rutsa da su kwanaki 47 suka wuce.

Sai dai Sanatan ya yi kira ga gwamnatin kasar China da ta shiga tsakani domin gaggauta ceto wadanda abin ya shafa.

Ya yi wannan jawabi ne a yayin ziyarar kwamitin hadin gwiwa na Majalisar Dokoki ta kasa kan sufurin jirgin kasan Legas zuwa Ibadan.

Dan majalisar, wanda ke wakiltar Oyo ta Arewa a Majalisar Dattijan, ya ce lamarin da ya faru a ranar 28 ga watan Maris, ya jefa shakku ga ’yan Najeriya da suka fara rungumar jirgin kasa a matsayin hanyar tafiye-tafiyensu.

Ya ce babu laifi idan gwamnatin kasar China ta taimaka wa Najeriya domin ceto wadanda lamarin ya shafa.

Aminiya ta rawaito cewa, titin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna mai tsawon kilomita 159, wani katafaren kamfanin gine-gine na kasar China, wato CCECC ne ya gina shi, kuma Bankin Kasar China ne ya bayar da kayayyakin titin.

Ya ce idan wadanda ke cikin dajin na bukatar lamuni, China za ta iya shige wa gaba, inda ya kuma bukaci hukumar CCECC da ta mika sakon ga gwamnatin kasar China don taimaka wa Najeriya.

Sanatan ya kara da cewa, idan har kasar China za ta iya taimaka wa kasar Rasha a yakin da ta ke yi da Ukraine, babu laifi wajen taimakon Najeriya a halin da ta ke ciki.

“Ina kira gare ku da ku taimaka mana, maimakon ku je China ku zo nan, tsaron rayukan wadanda abin ya shafa na da matukar muhimmanci.

“Bayan kwanaki 47, ‘yan uwanmu maza da mata suna hannun masu garkuwa, ku taimaka mana ku isar da wannan sako ga gwamnatin kasar China,” in ji shi.

Manajan aikin na CCECC, Xia Lijun, ya ce kamfanin na CCECC a matsayinsa na kamfanin gine-gine, ya zamanto mai cin gashin kansa daga gwamnatin China, ya kuma ce kamfanin ya damu matuka da lamarin harin da aka kai kan jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna.

Daraktan Ayyuka na NRC, Mista Niyi Ali, wanda ya wakilci Manajan-Darakta Engr. Fidet Okhiria, cewa ya yi hukumar na hada kai da jami’an tsaro domin ganin an sako wadanda aka sace yayin harin.