Dan kwallon tawagar Brazil, mai tsaron baya, Alex Telles ya koma taka leda a Al-Nassr daga Manchester United.
Telles, mai shekara 30, zai taka leda tare da tsohon dan wasan United, Cristiano Ronaldo, wanda ya koma buga babbar gasar Saudi Pro League a watan Janairu.
- Dalibai sun lakada wa malami duka saboda hana su satar jarrabawa
- Kasashen Musulmi sun fusata kan kona Al-Qur’ani sau uku cikin wata daya
Kungiyoyin biyu ba su fayyace kudin cinikin dan kwallon Brazil din ba.
Telles ya yi wasa 50 a United tun bayan da ta dauko shi daga Porto kan fam miliyan 13.6 a 2020, wanda ya yi wasannin aro a Sevilla a kakar da ta wuce.
A kakar bana, babbar gasar tamaula ta Saudi Arabia ta dauki fitattun ’yan kwallo, ciki har da Karim Benzema, wanda kwantiraginsa ya kare a Real Madrid.
Telles shi ne na baya-bayan nan daga Firimiyar Ingila da ya koma zai buga Saudi Pro League da ya hada da N’Golo Kante daga Chelsea da dan wasan Liverpool Roberto Firmino.
Telles, wanda ya yi wa Brazil wasa 12 da guda biyu a kofin duniya a Qatar a 2022, ya yi takarar buga gurbin lamba uku tare da Luke Shaw a Old Trafford.