✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

dan kwallon Super Eagles Ogenyi Onazi ya tsallake rijiya da baya a harin bam din Jos

daya daga  cikin ’yan kwallon Najeriya Super Eagles Ogenyi Onazi haifaffen Jos ya bayyana yadda ya auna arziki a harin bam din Jos na kwanakin…

daya daga  cikin ’yan kwallon Najeriya Super Eagles Ogenyi Onazi haifaffen Jos ya bayyana yadda ya auna arziki a harin bam din Jos na kwanakin baya.
Ya ce bayan ya ziyarci Jos don ganawa da iyalinsa jim kadan bayan ya samu hutu ne sai ya yanke shawarar ya ziyarci kasuwar da ake wa lakabi da Bus Terminal And Market amma a kasa da mintuna talatin bayan ya gama sayayya sai ya samu labarin bam ya tashi inda ya halaka akalla mutum 118.
“A gaskiya na auna arziki da yanzu haka sai dai labari”, inji Onazi.
Onazi wanda yake buga kwallonsa a kulob din Lazio da ke Italiya yanzu haka ya hadu da ’yan kwallon Super Eagles a shirye-shiryen da suke yi na tafiya gasar cin kofin duniya a Brazil.  Hasalima yana daga cikin ’yan kwallon da suka yi wa Eagles wasa a wasan sada zumunta da kasar Sukotlan a shekaranjiya Laraba a birnin Landan.