A ranar Juma’ar da ta wuce ce daya daga cikin ’yan kwallon Najeriya, Super Eagles Samuel Kalu ya yanke jiki ya fadi a sume yana tsakiyar kwallo saboda tsananin zafi a Masar.
Dan kwallon yana daga cikin ’yan wasan Eagles da ke samun horo ne a kokarin tunkarar wasansu na farko da Burundi da aka yi ranar Asabar inda Najeriya ta samun nasara a wasan da ci 1-0.
Hakan ya sa likitocin kungiyar suka garzaya da Samuel Kalu zuwa wani asibiti mafi kusa inda aka yi masa magani. Likitoci a asibitin sun tabbatar Kalu ya sume ne saboda tsananin zafi wanda hakan ya sa ruwan jikinsa ya yi kasa.
Samuel Kalu dan shekara 21 yana kwallo ne a kulob din Bordeaud da ke Faransa.
Mai magana da yawun kungiyar Super Eagles, Toyin Ibitoye ya tabbatar da aukuwar lamarin inda ya ce tuni dan kwallon ya murmure kuma ya ci gaba da yi wa kungiyar wasa.
Saboda wannan matsala Kalu bai buga wasan farko da Najeriya ta yi da Burundi a ranar Asabar da ta wuce ba.
Tsananin zafi ya sa Hukumar Shirya Wasan Kwallon Kafa ta Afirka (CAF) ta amince a rika tsayar da wasa na tsawon minti uku-uku a minti 30 da na 70 don ’yan kwallo su rika sararawa.
Rahoton da Sashin Afirka na harkar kwallo na gidan Rediyon BBC Africa ya kalato ya nuna tsananin zafi a Masar ya kai maki 40 a ma’aunin Celcius.