Rahotannin da ke fiowa daga Italiya sun tabbatar da cewa wani dan kwallo dan asalin Najeriya da ke Italiya mai suna King Paul Akpan Udoh ya kamu da cutar Kurona.
King Paul Udoh wanda haifaffen Najeriya ne yana buga kwallo ne a kulob din Pianese da ke wasa a Rukuni na Uku (Serie C) a Italiya.
Rahoton da kafar watsa labarai ta Naijanews.com ta kalato ya ce a ranar 27 ga Fabrairu ne aka tabbatar dan kwallon ya kamu da cutar bayan binciken da aka yi masa.
King Paul Udoh mai shekara 22 ya fara kwallo ne a kulob din Reggiana da ke Italiya a shekarar 2011 kafin ya koma kulob din Jubentus. Daga nan ne kulob din Jubentus ya bayar da shi aro na tsawon shekara daya ga wani kulob amma bayan shekara daya sai ya sake komawa Jubentus inda daga nan ne aka sayar da shi ga kulob din Pianese a ranar 14 ga Yulin bara.
Cutar Kurona dai ta mamaye sassan duniya ciki har da Italiya kasar da ake ganin kawo yanzu ta fi kowace kasa a Nahiyar Turai yawan wadanda suka kamu da cutar.