dan kwallon kafar kulob din Real Madrid da ke Sifen James Rodriguez ya samu rauni mai tsanani a jijiyoyin kafarsa ta dama da hakan zai sa ya shafe wani lokaci ba tare da ya buga wa kulob din kwallo ba. Kodayake kulob din bai ambaci takamaiman lokacin da dan kwallon zai shafe a zaune ba tare da ya yi wasa ba.
dan shekara 23, bai buga wasan da kulob din Madrid ya yi da na Ludogoret a gasar zakarun kulob-kulob na Turai (Champions League) a ranar Talatar da ta wuce ba saboda rashin lafiyar tasa.
Ya samu raunin ne a wasan da kulob din ya yi da na Celta bigo a gasar rukunin La-Liga na Sifen a ranar Asabar da ta wuce bayan kulob din na Madrid ya samu nasara a wasan da ci 3-0.
Tuni kocin kulob din Carlos Ancelotti ya tabbatar da jin raunin dan kwallon kuma ya ce ga dukkan alamu ba zai kara yin wasa ba sai a watan Janairu mai zuwa.
Kafin ya samu raunin, sai da dan kwallon ya buga dukkan wasanni 24 da kulob din ya yi a kakar wasa ta bana.
…dan kwallon Madrid, Rodriguez ya ji rauni
dan kwallon kafar kulob din Real Madrid da ke Sifen James Rodriguez ya samu rauni mai tsanani a jijiyoyin kafarsa ta dama da hakan zai…