Rafel Henzel, da ke buga wa kulob din Chapecoense na Brazil kwallo ya rasu bayan ya tsira daga hadarin jirgin sama da ya kashe fiye da mutum 70 shekara biyu da suka wuce.
Jirgin dauke da fasinjoji 77 ciki har da ’yan kwallon Chapecoense 19 na Brazil ya yi hadari ne a Kolombiya lokacin da mai ya kare masa inda mutum shida ne kacal suka tsira yayin da sauran suka hallaka bayan jirgin ya fado.
’Yan kwallon Chapecoense suna hanyarsu ta zuwa Kolombiya ne don buga wasan karshe a gasar cin Kofin Kalubale da wani kulob a Kolombiya amma hadarin ya rutsa da su.
Sai dai Rafeal yana daga cikin fasinjoji 6 da suka tsira.
Bayan da ya samu lafiya sai Rafeal ya yanke shawarar komawa gidan rediyo don ci gaba da aikin jarida. amma ranar Talatar da ta wuce, Rafeal mai shekara 45 ya gamu da ajalinsa jim kadan bayan ya tafi wani filin kwallo don buga kwallon kafa tare da abokansa.
Rahoton da kafar watsa labarai ta Sun Sport ta kalato ya nuna ana tsakiyar wasa Rafeal Henzel ya kamu da ciwon bugun zuciya, inda nan take ya fadi kuma kafin a garzaya da shi asibiti rai ya yi halinsa.
Takwarorinsa da suke wasa tare lokacin da lamarin ya faru sun yi matukar girgiza kuma tuni suka aika da sakon ta’aziyyarsu ga iyalan mamacin.
Yanzu Rafeal ya shiga sahun ’yan kwallon Chapecoense da suka rasu kimanin shekara biyu da suka wuce a hadarin jirgin sama sai dai shi a filin kwallo ya rasu.