✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dan kunar bakin wake ya kashe dan sanda a Pakistan

Dan kunar bakin wake ya tashi bam a cikin tasi.

Wani dan kunar bakin wake ya kashe dan sanda daya tare da jikkata wasu da dama a kasar Pakistan.

Babban jami’in dan sanda, Sohail Zafar Chattha, ya ce tun da farko sun zargi wani direban tasi wanda suka dinga bibiyar sa don ganin inda zai je.

“Da ya lura muna bin sa sai ya tsaya a wani waje, yana fitowa ya sake komawa ya danna bam din, nan take muka samu raunuka. Jami’inmu daya ya rasu,” in ji shi.

Yankin Islamabad ya samu sauki daga munanan hare-hare a baya-bayan nan, a yayin da yankunan Lahore da Karachi da ke makwabtaka da iyakar Pakistan da Afganistan ke fuskantar barazana hare-hare.

Pakistan dai ta sha fama da hare-haren bam da na kunar bakin wake, amma tsaro ya inganta tun bayan wani farmaki da sojoji suka kaddamar a kan ’yan ta’adda a 2016.