Shahararen mai wasan kokawar Turawa (Wrestling) Ultimate Warriors dan Amurka ya mutu a ranar Lahadin da ta wuce. Ya mutu ne a lokacin da yake da shekara 54.
“Hukumar da ke shirya gasar kokawar Turawa (WWF) ce ta sanar da haka ta bakin daya daga cikin kamfanin da ke daukar nauyin gasar mai suna Stamford Connecticut a kafar sadarwarsa a ranar Lahadin da ta wuce.
Shi dai marigayi Ultimate Warrior asalin sunansa shi ne James Hellwig. Ya fara gasar kokawar Turawa (Wrestling) ne a shekarar 1987 kimanin shekaru 27 da suka wuce.
Ya yi wasan kokawa ne tare da shahararrun ’yan wasa irin su Hulk Hogan da Randy “Macho Man” a lokacin da yake raye.
Ga masu sha’awar kallon kokawar Turawa sun san marigayin a matsayin mai yin zane a fuskarsa kamar dodo sannan yakan baza gashinsa kamar mahuakaci baya ga daure damtsensa da kyallaye.
Dan kokawar Turawa Ultimate Warrior ya mutu
Shahararen mai wasan kokawar Turawa (Wrestling) Ultimate Warriors dan Amurka ya mutu a ranar Lahadin da ta wuce. Ya mutu ne a lokacin da yake…
