Wani dan kasuwa mai shekara 50 mai suna Alhaji Lawan Garba da aka yi garkuwa da shi a kauyen Kwadabe da ke Karamar Hukumar Kiyawa a Jihar Jigawa, ya kubuta.
Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, DSP Lawan Shiisu Adam ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba a Dutse, babban birnin jihar.
- ’Yan Boko Haram sun kashe sojojin Chadi da dama a harin kwanton bauna
- Dalilin da ya sa Hawainiya ke sauya launin jikinta
A cewarsa, “An sako Alhaji Amadu Garba, wanda aka yi garkuwa da shi a ranar 21/11/2022 a wani daji kusa da kauyen Baranda a Karamar Hukumar Dutse.”
Sai dai ba a bayyana ko iyalan mutumin sun biya kudin fansa kafin a sake shi ba.
Kakakin ya ce rundunar ‘yan sandan jihar na kokarin ganin ta cafke wadanda suka yi garkuwa da mutumin.
Kazalika, ya roki jama’ar jihar da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro hadin musamman ta hanyar gabatar da bayanai da za su taimaka wajen dakile miyagun laifuka a fadin jihar.
Idan ba a manta a ranar Talata, Aminiya ta ruwaito yadda wasu maharan suka shiga gidan dan kasuwar suka sace.