Wani karin dan Jam’iyyar LP a Majalisar Wakilai, Daylop Chollom daga Jihar Filato ya sauya sheka zuwa Jam’iyyar APC.
A ranar Talata ne dan majalisar mai wakilatar Barkin Ladi/Riyom ya koma APC, kamar yadda shugaban Majalisar, Honorabul Abbas Tajuddeen ya sanar.
A cewar wasikan dan majalisar, ya yanke shawarar komawa APC ne bayan yin dogon nazari kan rikicin cikin gada da ya dabaibaye jam’iyyar LP a matakin kasa.
Ya kara da cewa dorewar ci-gaban mazabarta shi ne ya fi komai muhimmanci, don haka yake ganin za su fi samun romon dimokuradiyya idan yana cikin ja’iyya mai mulki.
- Me Tinubu ya yi da za a sake zaben shi —Atiku
- An yi garkuwa da hadimin Yahaya Bello
- Yadda dillalai ke zagon ƙasa ga shirin tallafin kayan noma
Sai dai kuma Shugaban Marasa Rinjaye na Majalisar Wakilai, Honorabul Kingsley Chinda ya bayyana sauya shekar a matsayin haramtacce, yana mai dogaro da Sashe na 68 (1) (d) ma kundin tsarin mulkin Nijeriya.
Chinda ya bukaci dan majalisar ya gabatar da shaidar ficewarsa daga LP, wanda shugaban majalisar ya tabbatar da cewa ya gani kuma ya gamsu.
Dagan dan Kingsley Chinda ya bukaci a kwace kujerar dan majalisar da ya sauya sheka, amma shugaban majalisar ya yi watsi da bukatar.
Shi ma Honorabul George Ozodinobi (Anambra, LP) ya bayyana takaicinsa yana mai cewa babu wani rikici a jam’iyyar.
Wannan dai na zuwa ne bayan a ranar Alhamis da ta gabata mutum hudu sun sauya sheka zuwa APC daga LP da kuma PDP a majalisar.
’Yan majalisa Tochukwu Chinedu Okere (LP, Imo) da Donatus Matthew (LP, Kaduna), da Akiba Bassey (LP, Cross River) da kuma Esosa Iyawe (LP, Edo) ne suka koma APC a wancan karon.
Ta biyar dinsu ita ce, Erhiatake Ibori-Suenu, ’yar tsohon gwamnan jihar Delta, James Ibori, wadda ta sauya shekar zuwa APC daga PDP.