Wani dalibi da ke matakin aji na uku a jami’ar kimiyya da fasaha ta Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi ya kashe kansa a ranar Juma’ar da ta gabata.
An gano cewa ya rataye kansa a sanyin safiyar ranar da lamarin ya auku inda hakan ya auku a bangaren makarantar da ake kira Gubi da ke kan hanyar Kano.
Marigayin mai suna Dahiru Adamu dan kimanin shekaru 30 dalibin sashen Ilimin kimiyya na katako ne.