✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dan Cristiano Ronaldo ya mutu

Cristiano ya tabbatar da mutuwar ne a shafinsa na Instagram

Daya daga cikin ’ya’ya tagwayen dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Cristiano Ronaldo, ya mutu.

Dan wasan ne ya tabbatar da mutuwar a wani sako da ya wallafa da yammacin Litinin a shafinsa na Instagram.

Sanarwar, mai dauke da sa hannun Cristiano da matarsa Georgina Rodriguez ta ce suna cikin dimuwa da jimami wanda ba su taba shiga irin shi ba.

“Cikin alhini muke sanar da rasuwar jaririnmu. Wannan wani yanayi ne na dimuwa da kowanne iyaye za su iya fadawa.

“Muna so mu yi amfani da wannan damar wajen gode wa likitoci da sauran ma’aikatan lafiya saboda gudunmawarsu.

“Muna cikin alhini, saboda haka muna bukatar sirri a cikin ’yan kwanakin nan masu wuyar sha’ani,” inji Cristiano.

Dama dai dan kwallon na da ’ya mai shekara hudu tare da matar tasa da ma wasu ’ya’yan.

Ko a ranar Asabar dai sai da ya buga wasan da kungiyarsa ta Manchester United ta fafata da takwararta ta Norwich, inda ya ci mata kwallo uku rigis a wasan.

%d bloggers like this: