✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dan Boko Haram dauke da makamai ya yi ‘saranda’ a Borno

Wani mayakin kungiyar Boko Haram ya mika wuya ga sojojin Najeriya da ke rundunar Operation Hadin Kai da ke Jihar Borno.

Wani mayakin kungiyar Boko Haram ya mika wuya ga sojojin Operation Hadin Kai da ke Jihar Borno.

Dan ta’addan da ya fito daga sansanin Boko Haram da ke Dajin Sambisa ya mika wuya ne ga sojojin Bataliya ta 112 da ke Mafa a ranar 28 ga Afrilu, 2024.

Hakazalika ya mika wa sojojin bindigarsa kirar Ak47 da alburusai da wayoyin salula uku da sauran kayayyaki.

Daga lokaci zuwa lokaci dai akan samu mayakan Boko Haram da ke mika kansu ga sojojin Najeriya sakamakon matsa wa sansanoninsu da sojoji ke  yi da luguden wuta.

Rikicin Boko Haram dai ya lakume rayuka da dama, musamman a jihohin Borno da Adamawa da Vobe, gami da raba dubban daruruwan jama’a da muhallansu.

Har yanzu dubban daruruwan muta da rikicin ya daidaita suna zaune a sansanoni gudun hijira, wasunsu ma a kasashen waje, wasu kuma sun bar mahaifansu.

Har yanzu daruruwan mutane da suka hada da mata da kananan yara da kungiyar  ta yi garkuwa da su ba su dawo ba.

A shekarar 2009 kungiyar Boko Haram ta fara tayar da kayar baya, kuma har yanzu ba a shawo kan masalar ba.