✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan A Daidaita Sahu sun kara kudin fasinja a Kano

Masu bumburuu na sayar da galan din feur a kan N5,000

Masu baburan A Daidaita Sahu a Kano sun yi karin kudin fasinja saboda tsadar man fetur inda masu bumburutu ke sayar da galan a kan N5,000.

Fasinjoji sun danganta karin kudin da aka samu da kimanin rabi kan wahalar man fetur da ake fama da ita a sassan Najeriya.

Wani fasinja mai suna Aminu Sadiq ya ce Naira 300 ya biya daga tsohuwar Jami’ar Bayero (BUK) zuwa titin Gidan Zoo, maimakon N200 da ya saba biya kafin yanzu.

Fatima Suleiman kuma Naria 100 aka caje ta kudin A Daidaita Sahu zuwa wurin da ta saba biyan N100.

Tashin farashin litar fetur zuwa sama na Naira 1,000 shi ne babban dalilin wannan tsadar kudin sufuri, a cewar fasinjoji.

Aminiya ta ruwaito cewa kudin A Daidaita Sahu daga Rijiyar Zaki Zuwa Zoo Road ya yi tashin gwauron zabo daga N300 zuwa N500.

Daga Sabuwar Jami’ar Bayero (BUK) zuwa Hotoro kuma kudin ya tashi daga N500 zuwa N1,000.

Aminiya ta gano cewa masu bumburutu sun koma sayar da galan guda na man fetur a kan N5,000.

Wakiliyarmu ta shida yadda ’yan bumburutu dauke da jarkoki suke kokawa da masu ababen hawa domin samun shiga gidajen mai.

Wadansu daga cikinsu sukan bayar da nagoro domin su samu man da suke zuwa su sayar da matukar tsada.

Aminiya ta yi kicibus da dogon layin ababen hawa a gidan man AY Shafa da ke unguwar Kofar Kabuga, duk kuwa da cewa ba sayar da man ake yi a gidan ba.