✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwamitin Binciken Ganduje Kan harkallar kadarorin gwamnati ya fara zama

Kwamitin shari'a da Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano ya kafa don binciken gwamnatin tsohon gwamna, Abdullahi Ganduje, ya fara zaman.

A yau Litinin ne kwamitin shari’a da Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano ya kafa don binciken gwamnatin tsohon gwamna, Abdullahi Umar Ganduje, ya fara zamansa.

An dora wa kwamitin shari’zai alhakin bincike kan zargin karkatar da kadarorin gwamnati da waus abubuwan da suka faru a mgwamnatin Ganduje na tsawon shekaru takwas.

Kwamitin karkashin jagorancin Mai Shari’a Faruk Lawan yana da mambobi da suka hada jami’an gwamnatin jihar, hukumomin tsaro, kungiyoyi masu zanan kansu da na ya kasuwa da sauransu.

Da yake jawabi game da kwamitin, Mai Shari’a Faruk Lawan Adamu ya bayyana cewa an dora wan kwamitin nauyin bincikar yadda aka sayar ko aka bayar da dukkanin wuraren da suke mallakar gwamnati jihar da kananan hukumomin jihar ne a ciki da wajen jihar Kano daga 2015 zuwa 2023.

Kwamitin zai jibici yada aka sayar ko aka mallaka wa wasu gonaki da makabartu da wuraren ibada da makarantu da sauransu.

“Kwamitin zai kokarin binciko wadanda aka sayar wa ko aka mallaka wa wurare; Za mu yi kokarin gano mutanen ko kamfaninka ko ma’aikatun da suka taka rawa cikin wannan sayarwa ko bayarwa da wadannan wurare.”
Justis Faruk Lawan ya bayyana cewa bayan sun kammala binciken za su fitar da shawarwari a kan duk wuraren.

Mai Shar’a Faruk ya kara da cewa ba a kafa kwamiyin don cin mutuncin kowa ba sai domin ya yi adalci’ a tsakanin al’ummar Jihar Kano.

Ya lashi takobin yin aiki bisa gaskiya da adalci don ba kowane bangare hakkinsa. Ya kuma nemi goyon bayan al’ummar Jihar Kano da su fito da duk wasu bayanai da za su taimaka wa Kwamitin wajen gudanar da aikinsa.

“Kofarmu a bude take ga duk maikorafi ko wani da yake da bayanai da zai taimaka wa kwamitin ya Aiko a rubuce inda za a neme shi daga baya don bayyana gaban Kwamitin tare da bayar da shaida akan bayanansa”