Rundunar ’yan sandan Jihar Imo ta ce ta bankado maboyar wasu masu garkuwa da mutane inda ta kashe daya daga cikinsu tare da ceto wani mutum da suka sace.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin ’yan sandan jihar, CSP Mike Abatam ya fitar a ranar Talata.
- Buhari ya umarci a gaggauta ceto duk daliban da aka sace
- Firimiyar Najeriya: Nasarawa United ta tunkudo Pillars daga mataki na biyu
Ya ce lamarin ya faru ne ranar Talata, daya ga watan Yulin 2021.
“Bayan sun hangi jami’an tsaro sai suka bude wuta, a wannan lokacin ne daya daga cikinsu ya kwanta dama, sannan ragowar suka tsere da raunukan harbi, sannan an ceto mutum daya cikin koshin lafiya.
“Daya daga cikin jami’an tsaron ya samu rauni, amma an garzaya da shi asibiti inda yake karbar kulawa daga likitoci.
“An samu babbar bindiga guda daya daga hannun bata-garin, sai kunshin harsasai guda biyar, sai salatif da suke daure mutanen da suka yi garkuwa da su.
“Mutumin da aka ceto ya bayyana wa ’yan sanda yadda suka kwace masa kudi N150,000, katin cirar kudi da sauran kayayyakin amfaninsa.
“An ajiye gawar dan bindigar a Cibiyar Lafiya ta Tarayya (FMC) da ke Owerri, sannan ana ci gaba da bincike don cafke wanda suka tsere da raunin,” cewar kakakin.