Ana fargabar kusan mutum 10 ne suka mutu bayan wani dan bindiga ya bude musu wuta a wani kantin sayar da kaya na Walmart da ke Chesapeake a Jihar Virginia ta Amurka.
Dan bindigar ya kai harin ne da daren Talata, lokacin da ake tsaka da hada-hada a kantin, lamarin da ya kai ga asarar rayuka, wasu da dama kuma suka jikkata.
- ’Yan Boko Haram sun kashe sojojin Chadi da dama a harin kwanton bauna
- Buhari ya kaddamar da sabbin takardun kudi
Jami’in Hulda da Jama’a na ’yan sandan Chesapeake, Leo Kosinski, ya shaida wa gidan talabijin na CNN cewa sun ziyarci wajen da misalin karfe 10:12 na dare, inda suka tarar da mutanen da aka harbe da kuma shaidar yin harbin.
Har yanzu dai babu cikakkun bayanai kan ainihin adadin mutanen da aka kashe saboda masu aikin ceto sun yi ta kokarin share kantin tsawon dare, kuma ’yan sanda na fargabar za a iya samun karin wasu gawarwakin.
Da farko dai ’yan sanda sun ce sun yi amannar mutanen da aka kashe ba su kai 10 ba.
Leo Kosinski dai ya ce an hakikance cewa maharin na cikin wadanda aka kashe, amma ya ce babu tabbacin ko wani jami’in tsaro ya mayar da martani ta hanyar yin harbi yayin harin.
Masu bincike sun ce dan bindigar na iya kasancewa ma’aikaci ko kuma tsohohn ma’aikacin kantin, wanda ya bude wuta a wajen.
Hukumomin birnin na Chesapeake dai sun bukaci mutanen yankin su kaurace wa kantin yayin da ake ci gaba da bincike a kan lamarin.
Matsalar tsaro ta ’yan bindiga masu bude wuta kan mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba na daya daga cikin manyan kalubalen da Amurka ke fuskanta a ’yan shekarun nan.