✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dan bindiga dadi ya kashe mutum 9 a Amurka

An yi nasarar hallaka shi jim kadan bayan aikata wannan danyen aiki.

Wani dan bindiga dadi ya bude wuta a kan jama’a a birnin Allen na Jihar Texas da ke Amurka, inda bayanai ke tabbatar da cewa ya yi sanadin mutuwar akalla mutane tara.

Dan bindigar wanda ya bude wutar a wani rukunin shaguna da ke dauke da mutane da dama da ke cefanen karshen mako, ya kuma jikkata karin wadanda tsautsayi ya rutsa da su.

’Yan sanda a birnin na Allen dai sun ce maharin wanda ya isa cikin wata karamar mota, an yi nasarar hallaka shi jim kadan bayan aikata wannan danyen aiki.

Hukumomin ba su kai ga samar da bayanai a kansa ba, sai dai sun tabbatar da kasancewarsa guda daga cikin gawarwakin da aka kwashe a wajen.

DW ya ruwaito cewa daga cikin wadanda ya kashe har da wasu kananan yara wadanda shekarunsu ba su wuce biyar ba.