Manya-manyan matsalolin da ke addabar Arewacin Najeriya na da dimbin yawa. Ciki akwai azzalumai, kuma sokayen shugabanni wadanda ba su amfana wa yankin wata tsiya ba.
Wani masanin tarihi, Dokta Aliyu Muhammad Muri, ya tambaya: wane amfani shugabancin Hausa-Fulani ya yi wa dan Arewa? Yara miliyan 16 na ta bara bisa tituna, miliyoyin ’yan mata tallace-tallace kawai ke gabansu, wai su tara kudi don a yi masu kayan daki, daga karshe, auren ba ya cika shekara uku cikin amana.
Akwai lokacin da kungiyar zawrawa ta Jihar Kano ta yi barazanar tara zawara kimanin miliyan daya don su yi zanga-zanga saboda kuncin da suke ciki.
Gwamnonin Arewa, duk da masifar talauci da mutanensu ke ciki, ba su da wata ajanda da ta wuce su tara mawaka da ’yan ma’abba su ba su kudi. Sun bar yankin cikin fitinar yunwa, kaskanci, bara, tallace-tallace da fitintinun siyasa da sunan addini.
Kwanaki an bankado Gwamnan Jihar Kano yana karbar na- goro, maimakon mutane su ba da hadin kai a gano gaskiya, sai aka shiriritar da abin, aka dauko ’yan taratsin siyasa su rika cin mutuncin Jafar Jafar, wai suna kare gwamna. Tambayata, ita ce, wace al’umma ce ke yin haka? Me ye laifin dan jarida don ya yi aikinsa? Kai da ke da gaskiya, me ya kai ka yin batanci? Ai me gaskiya ba ya fada, sai a bi hanyoyin doka a gane gaskiya ne, ko karya ne, amma don lalacewa a koma a dauko ’yan aji biyu na firamare ana soki-burutsu, cin amanar kasa ne.
Wai me shugabannin Arewa suka yi wa bangaren firamare? A Arewa fa, muke, babu abin da ya sauya. Cikowar azuzuwan na nan, rashin kayan karatun na nan; ba a horas da malamai, kuma albashinsu bai canza ba.
Duk rikicin addini da kabilanci da ake fama da shi a Arewa, talauci ne da jahilci ya kawo shi. Yau Arewa ta rikice. Birnin Gwari, Kaduna, Zamfara, Katsina, Filato, Adamawa da Taraba, Binuwai, ko’ina kisan jama’a ake yi. A sace, a karbi kudin fansa. Misalin baya-bayan nan, shi ne, na Hassana da Hussaina da ake garkuwa da su. An ruweaito barayin sun ki karbar Naira miliyan biyar, wai miliyan 80 suke so a ba su. Don Allah duk mai hankali da kishi, ta yaya zai goyi bayan wadannan azzaluman da ko tsaro ba su iya samarwa? Ba su iya kare rai ballantana dukiya; ba su iya kare mutuncin kowa. Duk da wannan ake samun wasu na tozarta duk wanda ya kalubalanci mutanen da ba sa iya komai.
’Yan uwanka na maula, na bara, na talla, na banga, wace izza gare ka? Wace kima ta rage? Dubi fa makwabtanka, kowa cikin wahala yake, amma kana surutai da bayar da alkalumman karya. Alkalumma suka wuce mutum ya shiga gari. Ziyarci birane da kauyuka, ka ga wahala. Wasu jihohin dubban dalibansu ke barin makaranta da sun je aji shida saboda ba su da kudin da za su biya WAEC da NECO. Wasu kuma ba su iya shiga jami’a saboda batun kudin. Da wannan har wani na da bakin yin magana?
Shiga unguwannin talakawa ka sha kallo, ka ga kaskanci da wulakanci, sannan sai ka tafi ka wasa gwaninka.
Duk wanda ya ce an ci gaba, ya duba makwabtansa gida 40, ya ga nawa ke da mahallin kansu, nawa ke iya ci da kansu, nawa ke da aikin kirki, nawa ke iya ganin likita, nawa ke da karatu, sannan ya yanke wa kansa hukunci.
Dan Arewa, ka sani, ko ka ki, ko ka so, dole sai mulki ya bar Arewa. Ya koma kila wurin Inyamurai. To ba ka da tsari irin na siyasa, kai inuwar giginya ce, ba ka da al’adun kishin jama’a. Nan kuka zo, kuna zagin shugabannin baya, to yanzu me aka yi? Babu abin da ake ba a yi shi a baya ba. Shugabannin Arewa, ba ku da rana. Shi ya sa ake kisan mutane a Zamfara, a Birnin Gwari, a Taraba, a Adamawa, a Binuwai. Shi ya sa ake bara, ake yunwa. Wai kai kawai burinka ka azurta kanka? Bayan miliyoyi na yawo cikin wahala? Wannan ce koyarwa da tarbiyar da ka samu?
To amma babu sakarkaru irin masu mara wa azzalumai baya. Sai ka ga an kama shugaba dumu-dumu yana cin hanci da rashawa amma sai wani talaka ya fito yana goya masa baya. Yin haka akwai takaici.
Talakawa a Arewa ku farka, ku dubi hagunku da damarku, ku ga me kuka samu, me ake maku. Ya batun kiwon lafiya, asibitoci nawa kuka samu? Ya batun magani, kyauta ake ba ku? Ya batun ilimi, kuna iya samu cikin sauki? Ya tsaronku. Wadannan su ne abubuwan da za ku duba, maimakon banga da siyasar ubangida da makauniyar siyasa. In ba ku yi haka ba, to za a wayi gari, mulkin ya koma Kudu, kuma su yi abin da suka ga dama.
Ga ’yan kudun nan, muna ganin su, muna kuma jin kalamansu, kuma mun san yadda suke mulki. Kai kishin kanka, ka sani Najeriya kasa ce daya, amma mutanen kudu, so suke a sauya kundin tsarin mulki, su mallake komai, su bar ka yadda kake, da ma ba a yi ma tanadi ba, saboda haka, za ka koma gidan jiya.
Zaben 2019, wata dama ce da bai kamata ka yi wasa da ita ba. Abin ba addini ba ne, domin da addini ne to da yanzu ka fi kowa wadata. Kada ka yarda a yaudare ka da addini, domin addini bai ce a wulakanta ba.
Kwamared Bishir Dauda Sabuwar Unguwa Katsina.