✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dan Abiola ya bukaci Buhari ya binciki ‘yadda aka kashe mahaifinsa’

Dan Abiola ya bukaci Buhari ya yi musu adalci wajen gano musabbabin mutuwar mahaifinsu.

Mista Abdul Abiola, daya daga cikin ’ya’yan marigayi Cif MKO Abiola ya roki Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya binciki yadda aka yi mahaifinsa ya rasu.

Matashin ya wallafa haka ne ta shafinsa na Twitter @AbdulMKO a ranar Talata.

Ya ce lokaci ya yi da ’yan Najeriya za su san gaskiyar lamarin da ya kai ga rasuwar mahaifinsa, ya kuma ce kamata ya yi shugaban kasa ya duba rumbun adana bayanai.

A cewarsa zai taimaka wa shugaban kasar wajen tona asirin mutuwar marigayi MKO Abiola, inda jaddada cewa irin wannan mataki ne kawai zai tabbatar da adalci.

“Lokaci ya yi da al’ummar Najeriya za su san gaskiyar abin da ya faru bayan zaben 12 ga Yuni, 1993 da kuma abin da ya yi samadin mutuwar MKO Abiola da Kudirat Abiola da sauran jarumai.

“Ina kira ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya duba ma’ajiyar tarihin kasarmu domin yi mana adalci,” in ji shi.

Kamfanin Dillacin Labarai na Najeriya (NAN), ya rawaito cewa Abiola ne ake kyautata zaton ya lashe zaben shugaban kasa na ranar 12 ga watan Yunin 1993, amma shugaban kasa na wancan lokacin, Janar Ibrahim Babangida ya soke zaben.

Amma Abiola ya bayyana kansa a matsayin shugaban kasa a wani abin da ake kira Epetedo, abin da ya sa daga bisani gwamnatin soja ta marigayi Janar Sani Abacha ta daure shi.

Shugaba Buhari ya karrama Abiola da lambar girmamawa ta GCFR, wadda shugabannin kasar Najeriya ne kadai suka kebanta da ita.

Buhari ya kuma ayyana ranar 12 ga watan Yuni a matsayin Ranar Dimokuradiyya maimakon ranar 29 ga watan Mayu da ake bikin a baya.