✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Damina: Kada ku yi saurin shuka —AFAN ga manoma

Shugaban kungiyar manoma ta kasa reshen Jihar Inugu Romanus Eze ya ja hankalin manoma da kada su yi gaggawar shuka saboda fara saukar ruwan sama…

Shugaban kungiyar manoma ta kasa reshen Jihar Inugu Romanus Eze ya ja hankalin manoma da kada su yi gaggawar shuka saboda fara saukar ruwan sama da wuri

Eze ya ce wannan ruwan ba ya jika gona har ta yi shuka, sai dai ya rage zafin iska da kuma kura.

“Sababbin manoma na irin wannan kuskuren, amma wadanda suka dade suna yi sun san irin wannan ruwan na wuri ba ma za a kira shi damina ba.

“Don haka kada ganin yayyafi mai karfi ya sanya manoma su fara shuka, don bata lokacinsu ne da kudinsu” in ji shi.