✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Damfara: An karbar wa mai POS N75,000 an ba ta ledar ruwa 5

A Jihar Legas, wani mutum ya damfari wata mai sana’ar POS, inda ya karbi N75,000 ya bar mata ruwan leda (pure water) guda biyar. Rahotanni…

A Jihar Legas, wani mutum ya damfari wata mai sana’ar POS, inda ya karbi N75,000 ya bar mata ruwan leda (pure water) guda biyar.

Rahotanni sun ce mutumin mai suna Victor dai ya yaudari matar mai suna Joy ne a shagon nata wanda ba a jima da bude shi ba.

Mai shagon da aka yi damfarar, Elizabeth Adetula, ta bayyana yadda dan damfarar ke zuwa shagonta inda yake gaya mata cewa yana shirye-shiryen bikinsa auren shi.

Ta ce, “A karshen mako, Victor ya same ni a shago inda ya nemi da in kawo masa kaya saboda shirye-shiryen bikinsa da yake yi.

“Wata daga cikin ma’aikatana ta kira ni a waya saboda yanayin babban kwastoma da Victor ke da shi , wannan ya sa na ba ta damar  cewa ta karbi lambarsa.

“Har magana ma na yi masa cewa ya tallata mu a wajen amaryarsa idan tana bukatar masu kwalliyar mata, ya amsa, daga nan sai ya nemi in zo shago domin mu samu mu tattauna.

“Daga baya dai ya fice daga shagona bayan ya fahimci cewar ba zai samu kudi ba.

“Mai tsaron shagon nawa ta bayyana cewa Victor ya nemi Joy da ta ba shi N75,000 shi kuma zai biya Naira dubu biyu a matsayin kudin caji, imda Joy din ta amince.

“Bayan ya karbi kudin daga hannun Joy sai ya bar mata wata leda a shagonta tare da cewa ta ba shi canjin Naira hamsin domin ya je ya siyo wani abu ya dawo a wani shago da ke kusa da su.

“Daga bisani sai Joy ta duba ledar da ya bari a nan ne ta ga ba komai face ledar ruwa guda biyar, da ta fihimci cew dai yaudara ce, nan take ta fito daga shagon duk da ana ruwan sama domin nemansa, sai dai sama ko kasa ba ta gan shi ba.

“Hakan ya sa ta yi kuka tare da zubar da kwalla wanda ita ma kanta ba za ta iya bayyana abun da ya faru ba, sai dai ina tunanin cewa ya yi amfani da asiri ne wajen yin wannan yaudarar, inji ta.

Adetula ta ce ta shigar da kara a ofishin ’yan sanda, sai dai kuma sun nemi da ta ba da N100,000 domin bin diddigin wanda ake zargin.

“Mun yi ta kokarin kiran lambar wayar da Victor ya bar mana amma wanda ke daukan wayar ba abun da yake mana bayan shirme,” inji ta.

Kakakin ’yan sandan Jihar, Benjamin Hundenyun ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce yanzu ana nan ana gudanar da bincike.

Ya ce “Mafi yawan masu aikata laifi su kan buya a duk lokacin da suka aikata miyagun laifuka, wannan shi ke wahal da hukumar ’yan sanda wajen kama su.”