Shugaban Hukumar Sadarwa ta Kasa (NCC), Farfesa Umar Garba Dambatta ya yaba kan yadda ake amfani da kimiyyar sadarwa a Najeriya da yadda take bayar da gudunmawa ga ci gaban tattalin arziki inda a yanzu ta kai kashi 13.86 cikin 100 na kudin shiga na GDP.
Dambatta ya bayyana haka ne a ranar Alhamis din makon jiya wajen taro na 12 na Najeriya a Intanet wanda Hukumar Bunkasa Kimiyyar Bayanai (NITDA) da ke karkashin Ma’aikatar Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani bisa sanya idon Hukumar NCC.
Taron wanda ya gudana a dakin taro na duniya da ke Abuja ya samu halartar Shugaba Muhammadu Buhari wanda ya kaddamar da dabarun tattalin arzikin zamani da yadda za a aiwatar da tsarin mayar da Najeriya kan turbar kasar da ke amfani da sadarwar zamani.
Dambatta ya ce yana sa ran matakin zai hada kan vangarorin gwamnati da masu zaman kansu wajen zurfafa farfado da sadarwar zamani da bunkasa kirkira ta gida don bunkasa juyin juya-halin masana’antu a Najeriya da bude kafar tattalin arzikin zamani da ake bukata.
Yayin da yake kaddamar da kundin dokar tattalin arzikin zamanin, Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da Dambatta cewa gudunmawar da vangaren kimiyyar sadarwa ke bai wa tattalin arzikin kasa ya kara nuna irin muhimmancin fadada tattalin arziki.
Shugaban Kasar ya bukaci hukumomi a Ma’aikatar Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani su ci gaba da gudanar da ayyukan da suke yi don bunkasa tattalin arziki.
Shugaban Kasar ya ce ya zama wajibi ma’aikatar ta wayar da kan jama’a kan tsarin kare kididdiga ta kasa.
Babbar mai jawabi a taron, Misis Funke Opeke, Babbar Jami’ar Kamfanin Mainone Cable ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta fitar da cikakken tsari da dabaru don bunkasa kayayyakin aiki tare da cire duk wani shinge da ke yin tarnaki ga ayyukan kamfanonin sadarwa kamar haraji mai yawa da dokoki masu tsauri don kara samar da guraben ayyukan yi don bunkasar sadarwar zamani.
Opepe ta fada wa Shugaban Kasa da sauran mahalarta taron cewa “Ya zama wajibi Najeriya ta tabbatar masu ruwa-da-tsaki sun bi ka’ida don samar da guraben ayyukan yi tare da tabbatar da ganin ’yan Najeriya ba su zama masu amfani da kayayyakin kimiyya da ake shigowa da su kasar nan ba.
Opeke ta shawarci ’yan Najeriya cewa akwai bukatar tsarin bayar da tukuici don tabbatar da kamfanoni kirkirar kimiyya da fasaha masu tasowa sun ci gaba da dorewa. Ta bayar da shawarar bude ofishin tattalin arzikin zamani a kowane yanki na kasar nan. Ta bayar da tabbacin cewa tattalin arzkin zamani zai samar da karin Naira tiriliyan biyu ga tattalin arzikin kasa cikin shekara hudu masu zuwa.
Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Dokta Isa Ali Pantami ya yi magana kan nasarorin da ma’aikatar ta samu tun lokacin da ya kama aiki. Hakan ya hada da kafa karin cibiyoyin sadarwa na gaggawa wadanda Hukumar NCC ta gina bisa umarnin Gwamnatin Tarayya.
Pantami ya ce kimanin gine-gine 300 na Hukumar Aika Wasiku ta Kasa da ke fadin kasar nan za a sake gyarawa tare da amfani da su don samar da kudin shiga ga gwamnati.
Pantami ya ce ma’aikatar ta yi hadin gwiwa da Cibiyar Nazarin Kimiyya da Shirin Koyar da Sana’o’i da ke birnin Massachusetts.
Pantami ya bayyana alakar da ke akwai tsakanin ma’aikatar da Hukumar NCC wadda hakan ya kai ga rufewa ko amfani da layukan da ba a yi musu rajista ba da suka kai miliyan tara wadanda da dama daga cikin su vatagari ke amfani da su wajen tafka ta’asa.
Taron ya samu halartar Shugaban Majalisar Dattawa, Dokta Ahmad Lawan wanda Sanata Oluremi Tinubu, Shugabar Kwamitin Sadarwa ta wakilta da wakilin Shugaban Majalisar Wakilai da Gwamnan Jihar Nasarawa, Alhaji Abdullahi Sule da shugabannin ma’aikatu da hukumomin gwamnati da wakilan hukumomin kasashen waje.