✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Damawa a harkokin kudi: Masu ruwa da tsaki sun doshi karin mutum miliyan 2.6

Burin Najeriya na  samun kashi 80 cikin 100 suna shiga ana damawa da su a harkokin kudi nan da shekarar 2020 ya samu karin tagomashi…

Burin Najeriya na  samun kashi 80 cikin 100 suna shiga ana damawa da su a harkokin kudi nan da shekarar 2020 ya samu karin tagomashi a ranar Juma’a 14 ga Disamba 2018, lokacin da Kungiyar Inganta Sababbin Dabarun Damawa a Harkokin Kudi (EFInA) ta fitar da rahotonta na shekarar 2018.   Rahoton ya nuna cewa kashi 63.6 cikin 100 na ’yan Najeriya baligai yanzu suna hulda da bankuna da shiga hada-hadar kudi, yayin da kashi 36.6 ne kadai ba sa hulda da banki ko cibiyoyin hada-hadar kudi.

Kungiyar EFInA, kungiya ce mai zaman kanta da Hukumar Bunkasa Kasashe ta Birtaniya (DFID) da Gidauniyar Bill & Melinda Gates suke tallafa mata don fadada tsoma jama’a a harkokin banki da kudi a Najeriya.

Binciken na kungiyar da ke gudana duk bayan shekara biyu, yana gano yadda al’amura suke game da damawa a harkokin kudi a kasar nan.

Kafin Kungiyar EFInA ta fitar da rahoton na 2018 sai da ta gudanar da bincike a jihohi 36 na kasar nan ciki har da Birnin Tarayya Abuja. A kowace jiha kungiyar ta ji ra’ayin akalla mutum 750 inda ta samu nasarar tambayar kimanin mutum dubu 27 da 470 ko kashi 97 daga cikin 100 na mutanen da ta yi niyyar tuntuba da yawansu ya kai dubu 28 da 380.

Binciken ya yi la’akari da fannoni da dama da suka hada da yawan bankuna, karbar kudi da yawan ajiya da yawan karbar bashi da kuma yadda ake yawan gudanar da harkar banki a lunguna da kowane sako na kasar nan da sauransu.

Rahoton ya nuna an samu karuwar kashi 1.4 na masu hulda da banki a tsakanin shekarar 2016 zuwa 2018- sai raguwar karbar kudi  da kashi 2.2 a shekara biyun da kuma raguwar masu ajiya a bankuna da kashi 6.7 a wannan tsakani. Ma’aunan biya da karbar kudin shiga da ejan-ejan na bankuna duk sun samu karuwa da kashi 3.4 da kashi 1.3 da kuma kashi 0.6 bi da bi, yayin da kuma karbar basussuka a banki yana nan yadda yake na kashi 1.3 a tsakanin lokacin.

Rahoton ya nuna yadda aka samu raguwar kashi 1.6 daga kashi 30.1 a shekarar 2016 zuwa kashi 28.5 a shekarar 2018 a bangaren ’yan fensho da kuma yadda ake ajiya a wasu hanyoyin hada-hadar kudi ba banki ba, da kuma yadda ake huldar kudi ta hanyar wayar hannu ko ta ejan-ejan na bankuna da ke shiga kowane lungu da sako don yin hada-hadar kudi da al’umma da bangaren inshora da kuma ajiya da karbar kudi a bankuna.

Rahoton da EFInA ta fitar ya ce abubuwa uku ne suka fi kawo cikas game da samun nasarar hada-hadar kudi a Najeriya da suka hada da talauci da rashin wayewa da kuma rashin isassun rassan bankuna ko na hada-hadar kudi a kowane lungu da sako na kasar nan.

Rahoton ya gano kimanin ’yan Najeriya miliyan 60.1 ne ba su da asusun ajiya a banki, yayin da kimanin miliyan 96.3 ba su taba yin huldar banki a wayar hannu ba sannan kimanin miliyan 97.9 ne ba su da inshora.

A fannin amfani da na’urar zamani da ake yi, rahoton EFInA ya bayyana cewa, an rage amfani da tsabar kudade wajen yin hada-hadar kudi saboda amfani da  wayoyin hannu. A cewar EFInA ya ce, ’yan Najeriya miliyan 60.1 ba su da asusun ko ba su amfani da asusun ajiyar banki, yayin da miliyan 96.3 ba su amfani da wayar hannu a hulda da bankuna, kuma miliyan 97.9 ba su da ishora.

Game da amfani da sadarwar zamani a kasar nan, rahotan na EFInA ya bayyana cewa, duk da cewa suna da amfani wajen tsoma jama’a a  harkokin kudi, rahoton ya gano cewa yayin da ’yan Najeriya miliyan 35.5 ke amfani da asusun banki, (kashi 36.6 cikin 100 na baligai) wato baligai miliyan 3 kadai ne suke amfani da na’urar sadarwa da asusun banki wajen harkokin banki, yayin da ’yan Najeriya miliyan 60 ba su amfani da hanyar sadarwar zamani ko asusun banki.

Nazari ya nuna cewa, kashi 82 cikin 100 na baligan Najeriya da ya hada da manoma da kananan ’yan kasuwa suna karbar kudin shigarsu hannu da hannu yayin da kashi 10 cikin 100 suke karbar kudadensu ta hanyar sadawrwar zamani ko ta asusun banki, sai kuma kashi 8 cikin 100 ba sa karbar kudin ta duk hanyoyin.

Asusun ajiya a kasar ya fadi da kashi 13.3 cikin 100 a cewar rahotannin yayin da ajiyar kadarori da dabbobi ya kai miliyan 47.4 zuwa miliyan 54.7 tun a shekarar 2016. Wasu abubuwan koma baya da aka samu sun hada da rancen kudade inda suka kai kasa da kashi 2.0 cikin 100 da kudin da ake biya da ya kai kashi 1.0 cikin 100.

A kan ajandar hada-hadar kudade rahotanni sun ce, matasan Najeriya kashi 99.6 cikin 100 maza da suka kai kashi 33.5 cikin 100 ne suke harkar hada-hadar kudaden idan aka kwatanta da jinsin `yan mata da suke da kashi 29.4 cikin 100.

Wannan yana wakiltar koma baya da ya kai kashi 4.3 cikin 100 da 5.7 cikin 100 a jinsin maza da mata, da kuma samun koma baya da kashi 4.8 cikin 100 na adadin shekarar 2016 a duk jinsin.

A fannin hada-hadar kudade na rukunin shekaru rahotanni na bayyana adadin shekarun da ya kai daga shekaru 36 zuwa 45 (daidai da ‘yan Najeriya miliyan 19.5 da kuma kashi 30.6 cikin 100 da ba sa cikin tsarin) suna da da damar hadahadar kudade fiye da sauran. Wadannan rukunin suna cikin rukunin shekarun 26 zuwa 35 (daidai miliyan 30.3 da kuma kashi 31.5 cikin 100 na wadanda basa cikin tsarin) da rukunin shekaru 46 zuwa 55 (daidai da mutum miliyan 10.9 da ke da kashi 32.4 cikin 100 wadanda basa cikin tsarin)

Wadanda ba sa cikin tsarin a tsakanin birane da karkara na nuna kashi 21.6 cikin 100 na  `yan Najeriya a birane ne kawai ba sa cikin tsarin, idan aka kwatanta da wadanda suke karkara da suke da kashi  45.6 cikin 100.

Wannan na nuna alamar koma baya na kashi 2.8 cikin 100 da kashi 6.6  cikin 100 na wadanda ba sa cikin tsarin a yankunan birane da karkara. An samu jumullar kashi 4.8 cikin 100 tun shekarar 2016.

A tsakanin shiyyoyin Najeriya, Kudu maso Yamma da Kudu maso Gabas, suke da karancin marasa hada-hadar kudade a bankuna a baya, amma ba su yi bajinta ba, a shekara biyu da suka gabata. Shiyyoyin suna da kashi 18 cikin 100 da kashi 28 cikin 100 a shekarar 2016, idan aka kwatanta da shekarar 2018 inda suke da kashi 19 cikin 100 da kashi 29 cikin 100 na wadanda ba sa cikin tsarin.

Amma sauran bangarorin sun samu gagarumar raguwar nasarar shiga a dama da su a harkokin banki a shekara biyu da suka gabata, inda yankin Kudu maso Kudu ya samu ci gaba, daga kashi 31 cikin 100 zuwa kashi 23 a shekarar 2018, sai  Arewa ta Tsakiya ta dawo kashi 31 a bara daga kashi 39 a shekarar 2016. Yankin Arewa maso Gabas ya koma kashi 55 a bara maimakon kashi 62 a shekarar 2016 sai Arewa maso Yamma ta koma kashi 62 a bara maimakon kashi 70 a shekarar 2016.

Jadawalin yankunan ya  nuna cewa Jihohin Kano da Jigawa da Katsina a Arewa maso Yamma sun kasa cimma matsakaicin adadin  kashi 62.4, inda Kano take da mafi yawan marasa amfani da bankuna da kashi 75.2. Jihohin Gombe da Bauchi da Yobe sun gaza a yankin Arewa maso Gabas na kashi 54.5. Misali Jihar Gombe ce ke da kaso mafi girma na marasa hulda da banki da 76.1, sai Bauchi kashi 60.8 sai Yobe mai kashi 60. Jihar Taraba ce karancin marasa hulda da bankuna a yankin da kashi 30.9.

Jihohi 4 a Arewa ta Tsakiya sun kasa samun mafi karancin kason yankin na 30.6. Jihar Nasarawa ce ke kan gaba da marasa hulda da banki da kashi 39.5, sai Neja mai kashi 38.1 sai Filato mai kashi 37.8 da kuma Abuja mai kashi 31.9.

A Kudu maso Gabas, Jihar Ebonyi ta gaza cimma mafi karanci marsa hulda da banki na (kashi 29.9), inda take da kashi 43.6.

A yankin Kudu maso Kudu, jihohin Bayelsa da Akwa Ibom da Edo sun samu sama da kason yankin na 22.7 na marasa hulda da banki. Bayelsa na da kashi 35.3 sai Akwa Ibom kashi 29.1, sai Edo tana da kashi 25.4.

A yankin Kudu maso Yamma inda mafi karancin kason yankin yake 19.1, jihohin Ondo da Oyo da Ogun nuke da kaso mafi girma na kashi 28.8, da 22.8 da kashi 21.8 a jere. Osun ce ta samu nasarar zama mai karancin marasa hulda da banki da kashi 14.6 ba a yankin kadai ba, a kasar nan baki daya kamar yadda rahoton EFInA ya nuna.

A takaice, rahoton EFInA ya nuna cewa mutanen Najeriya miliyan 36.6 (mutum miliyan 63 da suka samu damar shiga harkokin kudi), yanzu ba sa hulda da bankuna maimakon mutum miliyan 56.9 a shekarar 2016. A cikin wadannan mutane, rahoton ya nuna cewa mata ne kashi 55.9 sannan maza ke da kashi 44.1. sannan rahoton ya kara da cewa mutanen Najeria masu shekara 18 zuwa 25 su ne suka fi yawa da kaso 34. Sannan a kauyuka akwai kashi 78.5, sai birane na da 21.5. sannan yankunan Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabas su ne yankunan da ke kan gaba a marasa hulda da bankuna .

Rahoton ya nuna cewa Naira 15,000 a matsayin kudin shiga da ‘yan Najeriya miliyan 99.6 ke samu, a yayin da kashi 71.3 cikin dari na adadin wadannan mutane ba su da asusun ajiya na tafi da gidanka, sannan kuma kashi 17.5 cikin dari ne na ‘yan Najeriya ke iya amsar bashin banki.

Wasu daga cikin abubuwan da rahoton ya gano sun hada da cewa, guraben aiki da sun yi kadan a kasar, ta yadda wadanda suka kammala jami’a ba su iya samun aiki, wanda haka ya sanya ake samun karacin kudin kashewa ga irin wadannan mutane, kuma hakan ke rage kudaden da ake adanawa a bankuna. Haka kuma an lura da yadda matasan Najeriya suka koma gudanar da kananan sana’o’i don su rayu. Wannan ne ya kara tabbatar da cewa abin da mutum zai kashe yau da kullum ne abin damuwa, don haka babu wani buri na ajiya don maganin matsalar gaba. Kungiyar EFInA ta fahimta da cewa an samu karuwar matasan da suka dogara da hanyoyin samun kudin shiga na kai tsaye, inda suke tu’ammali da tsabar kudi, wato ba tsarin tasarrufin banki ba.

Tun daga lokacin da aka kaddamar da Tsarin Bai Daya Na Harkokin Kudi Na Kasa a 2012, mutane sun tsaro hanyoyi daban-daban domin gudanar da harkokinsu na tu’ammali da kudi. An kakkafa kwamitoci daban-daban a jihohi a Janairu 2015 tare da kungiyoyi da kafafen fadakarwa dangane da al’umar kudi.

Haka kuma Babban Bankin Najeriya (CBN) ya kirkiro wani shiri mai taken Ka San Abokan Huldarka (KYC) a 2013 domin saukaka wa mutane masu matsakaitan hanyoyin samun kudin shiga su bude asusun ajiya na banki. Haka kuma an samar da ejan-ejan su kai tsare-tsaren kusa da jama’a, musamman kantunan sayar da magani, gidajen mai da manyan kantunan zamani su rika gudanar da bankin tafi-dagidanka a madadin tsayayyun bankuna.

Haka kuma, Hukumar Kula Da Katin Dan Kasa (NIMC) ta ci gaba da samar da katin dan kasa ga al’ummar Najeriya, a yayin da ita ma Hukumar Kula Da Tsarin Fensho ta Kasa ta ci gaba da tafiyar da nata tsari ga kamfanoni masu zaman kansu da cibiyoyin gwamnati da ma daidaikun mutane da ke tafiyar da harkokin kudi na kashin kansu.

Haka kuma, a yayin hadin gwiwa da masu ruwa da tsakinta, Hukumar Kula da Hannayen Jari (SEC) ta aiwatar da fara shirin kara samar da yawan cibiyoyin rabarwa don bunkasa hanyoyin yawan hada-hadar kudin kasuwar kayakin da muke samarwa, ta fuskar inganta illarin tsarin zuba jari da yawan kudaden kasuwancin da kuma dabarun bunkasa tattalin arziki.

Ita ma a bangarenta, Hukumar Inshora ta Kasa (NAIC) ta kaddamar da tsarin kayayyakin da babu ruwa cikinsu don samun damar kaiwa ga al’umma da yawa, musamman ma fito da mahajar bayani game da tsarin kananan inshore na kamfanoni ga masu juya su.

Haka kuma tsarin Bancassurance Framework wani bangare ne na bunkasa dukkan tsare-tsaren da aka shigar. Babban Banki CBN da NAICOM ne suka fitar da bayanan, a matakin da take dauka na fadada kwarin gwiwar inshora ga wadanda suke da asusun ajiyar banki.

A kwanan nan ma akwai wani hadin gwiwa da kuma hobbasa da aka gabatar don kara shigo da masu kamfanonin wayoyin sadarwa ta fuskar inganta hada-hadar kudi tsakanin masu amfani da ayyukan.

Haka kuma an hada hannu da ma’aikatun gwamnati don yin amfani da tsarinsu wajen habaka hada-hadar kudade tsakanin ak’umma a fadin kasar nan. Har’ila yau, CBN ya fitar da yadda ake amfani da tsarin jujjuya harkokin biyan kudi na bankuna (PSB a Najeriya.

A lokacin da shirin ya kankama nan gaba kadan a farkon wannan shekarar, zai samar da cikakken tsarin biyan kudade na dukkan ayyuka ta hanyar sadarwa. Wannan dauki ya taimaka gaya wajen samuwar cigaban da aka samu cikin rahotan EFInA.

Gyararren Tsarin Dabarun Hada-Hadar Kudi an fidda shi ne a Watan Nuwambar 2018. Inda masu ruwa da tsaki suka tsara hanyoyin dauki don cimma nasarar samar da hanyoyin kudi ga mata da matasa da mutanen karkara, da kuma kungiyoyin wasu yankun Arewacin kasar nan. Wannan don tabbatar da cewa an samu cikakken tsarin da za a soma al’umma cikin hada-hadar kudade.