✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

…Dalung bai ji dadin yadda aka yi wa kungiyar U-23 rikon sakainar kashi ba

Ministan matasa da wasanni Barista Solomon Dalung ya nuna rashin jin dadi a game da yadda Hukumar kwallon kafa ta kasa (NFF) ta yi wa…

Ministan matasa da wasanni Barista Solomon Dalung ya nuna rashin jin dadi a game da yadda Hukumar kwallon kafa ta kasa (NFF) ta yi wa kungiyar kwallon kafa ta ’yan kasa da shekara 23 (U-23)  rikon sakainar kashi a sansanin horar da su a Amurka a shirye-shiryen tunkarar gasar Olamfik da za a fara yau a Brazil.
Ministan ya koka ne a kan yadda hukumar ba ta samar wa ’yan kwallon masauki mai inganci ba da wajen samun horo da kuma yadda ta kasa biyan su alawus don tafiyar da harkokinsu na yau da kullum.
Ministan ya bayyana wadannan koke ne a ziyarar da ya kai wa ’yan kwallon a ranar Litinin da ta gabata a Amurka a sansanin horar da su kafin su wuce zuwa Brazil don halartar gasar wasanni ta Olamfik da aka fara yau.
“Ban gamsu da yadda Hukumar NFF ta yi wa ’yan kwallon tanadi a sansanin horar da su a Amurka ba, hasalima ma’aikatar matasa da wasanni ba ta da masaniya a kan haka sai yanzu da na gani da idona a ziyarar da na kawo”.
Idan za a tuna, a karshen makon jiya wasu kafofin watsa labarai sun ruwaito cewa Kyaftin din tawagar Najeriya a gasar Olamfik John Obi Mikel ne ya ba ’yan kwallon tallafin Dala dubu 30 kwatankwacin Naira Miliyan 10 saboda halin ni-’yasun da suka tsnci kansu a ciki.  Amma daga baya Mikel din ya karyata rahoton, sai dai duk da haka masana harkar kwallo sun tabbatar akwai matsala a yadda hukumar ta yi wa ’yan kwallon rikon sakainar kashi.
Hakan ya sa ake hasashen da wuya ’yan kwallon su taka rawar gani a gasar Olamfik ta bana, ganin tun ba a je ko’ina ba sun fara fuskantar matsala.
 Kimanin shekaru 20 kenan (1996) da kungiyar kwallon kafa ta U-23 ta samu nasarar lashe lambar zinare a bangaren kwallon kafa a gasar Olamfik da ta gudana a Atlanta ta Amurka, don haka a wannan karo ana ganin da wuya kungiyar ta samu irin wannan nasara ganin ta fara fuskantar matsala ne tun ma kafin a fara gasar.