Duk shekara hukumomin kasar Saudiyya kan dage rigar Ka’aba (Kiswah) sannan a lullube ta da farin kyalle kafin a fara aikin Hajji.
Ana lullube Ka’bah da farin kyallen ne domin alamta cewa shi ma ya dau harama (ya sa haramin aikin Hajji), wato an shiga lokacin aikin Hajji.
Akan dage Kiswah na tsawon mita uku takaninsa da kasa a kowace shekara domin kare shi daga lalacewa sakamakon alhazan da ke yin dawafi a Masallacin Harami a lokacin Hajji.
Miliyoyin alhazan da ke shiga Masallacin Harami a kai a kai domin yin dawafi ba zai yiwu a iya tare su domin kare rigar Ka’abah ba cikin sauki.
Ana kuma dage Kiswah ne saboda wasu masu camfi daga cikin alhazai da ke yankarsa domin amfani da shi domin neamn wata falala. Haka kuma akwai masu rubuta addu’o’i ko sunayensu a jiki da tunanin samun falala.
Yadda aka sa wa Ka’abah farin kyalle
Ana sa wa Ka’abah farin kyalle ne domin nuna alamar shigar lokacin aikin Hajji.
A da can akan dago ta ne daga kasa a rataye ta sama a jikin Ka’abah ta yadda farin da ke ta cikin Kiswan ke bayyana .
Amma shekarun baya-bayn nan ana amfani ne da farin kyalle na daban domin lullube Ka’abah idan lokacin ya yi.
Ranar da ake dage Kiswah
An saba dage Kiswah da sa farin kyalle a ranar15 ga watan Dhul Qidah ko kuma kwana daya kafin ko bayanta.
Dalili shi ne bayan 15 ga wata ne alhzai ke fara yin tururuwa a Harami domin yin dawafi, ba dare ba rana.
Saboda haka zai yi wuya a iya dage Kiswah cikin sauki a idan aka bari zuwa lokacin da alhazai suka fara dawafi.
Babu dage Kiswah ranar 15 ga Dhul Qidah a bana
Amma bana (2020) Ma’aikatar Aikin hajji da Umarah ta kasar Saudiyya ta ce ba za a dage rigar Ka’aba ba kamar yadda aka saba.
Kasar ta takaita yawan alhazai zuwa kimanin 10,000 sakamakon cutar coronavirus, don haka take ganin ba za a samu cinkoson mutane sosai ba a wurin dawafi.
Saboda haka bana sai ranar 1 ga watan Zul Hajji za a dage Kiswah, kuma ana tunanin aikin zai zo da sauki saboda karancin alhajizai.
Dokokin aikin Hajji a lokacin COVID-19
Saudiyya ta kuma takaita aikin Hajjin bana zuwa ga mutanen da ke cikin kasar kadai, domin dakile yaduwar cutar COVID-19 a tsakanin mutane ko jefa su cikin hadarin kamuwa a lokain aikin Hajji.
Haka kuma ba za ta bar ‘yan shekaru fiye da 65 ba da masu cututtuka masu tsanani su halarci ibadar.
Za kuma a yi wa maniyyata cikakken gwajin coronavirus na wajibi kafin su fara aikin Hajji.
Kullum kuma sai an yi musu gwaji a tsawon kwanakin aikin Hajji.
Wajibi ne kuma a rika bayar da tazara a kowace gaba ta aikin Hajji.
Bayan kammla aikin Hajji za a killace su kafin a bari su koma cikin jama’a.