✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin mai da ni saniyar ware —Zainab Buba Galadima

Na tabbata wasu abubuwan da ake yi Buhari bai sani ba

Zainab diyar makusancin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari wanda yanzu suka raba jiha, Buba Galadima ce.

Tsohuwar Hadima ta Musamman ce ga Mataimakin Shugaban Kasa kan Ayyukan Muradun Cigaba Mai Dorewa (SDGs) a wa’adin farko na Shugaba Buhari.

A wannan hirar ta musamman, ta bayyana wa Aminiya abin da ta fuskanta a Fadar Shugaban Kasa, alakar gidansu da iyalan Buhari da abin da ya sa mahaifinta da Buhari suka bata.

 

Kin yi aiki a matsayin Hadima ta Musamman a Ofishin Mataimakin Shugaban Kasa, yaya za ki bayyana yadda aikin ya kasance?

Yana daga cikin kalubale mafi girma a rayuwata. Na fuskanci takura saboda abubuwan da suka faru sun sa ni cikin damuwa.

Mutane na ganin ina aiki a Fadar Shugaban Kasa amma ba a biya na albashi.

Takardar daukar aiki ma ba ni da ita sai da na kammala wa’adina na kansila a Birnin Tarayya, saboda haka ga ni nan dai.

Sai a 2017 aka ba ni takardar daukar aiki amma ba ta da bambanci da takardar tsire; Mataimakin Shugaban Ma’aikatan Shugaban Kasa, Abdul Rahman Ikpaye ne ya sa mata hannu amma ba a ayyana ayyukana ba.

Dalilin, a cewarsu, shi ne ba za mu yi aiki a karkashin gwamnati ba sai dai mu samo hukumomin jinkai da za su dauki nauyin shirin da muke karkashi.

Tsakani da Allah an musguna min, na ga wulakanci da abin takaici.

 

Shin kina ganin sukar gwamnati da mahaifinki ke yi ne ya sa kika fuskanci hakan?

Haka ne, saboda ai mu mutane mukan yi wa wasu hukunci gwargwadon tunaninmu game da su.

Kawai don ka hada dangantaka da mutumin da suke ganin abokin adawarsu ne sai su yanke maka hukunci, wannan ma ta faru da ni sosai.

 

Yaya kika ga martanin ’yan-a-mutum Buhari game da yawan sukar da mahaifinki ke yi?

Kowa da irin nashi. Wasu na mutunta hakan da cewa ra’ayinsa yake bayyanawa, wasu kuma na daukar sa makiyi.

Sai da ta kai wani yaron mahaifina ya jagoranci neman ganin an kore ni daga Fadar Shugaban Kasa, amma Mataimakin Shugaban Kasa na so na.

Duk da haka mutumin ya rika bin wasu hanyoyi da yake da iko da su don cimma manufar tasa.

Sai da ta kai ana hana ni shiga Fadar Shugaban Kasa sai na kira wani babban jami’in tsaro kafin a bari in shiga; an kuma hana ni katin izinin shiga Fadar Shugaban Kasa kai tsaye.

Lokacin da mahaifina ya fara R-APC aka ba ni katin amma kafin lokacin sunana na cikin jerin matunen da aka sanya sunayensu a matsayin masu shiga babbar kofar Villa na dindindin.

Da na zo kofar zan tsaya a tantance ni in shiga, amma wata rana da na zo sai kwatsam na iske an cire ni a jerin sunayen.

 

Shin akwai wasu abubuwa kuma daga aka hana ki?

Ba a taba biya na albashi ko alawus ba. Ina dai nan ne kawai.

 

To yaya kike rayuwa?

Ina da rufin asiri daidai gwargwado da ba sai na dogara da abin da gwamnati ta ba ni ba. Na san ko ba ni da kudi ba zan zauna da yunwa ba, saboda ina da ’yan uwa da abokan arziki.

 

Shin bayan cikar wa’adin aikinki an ba ki kudin sallma?

A’a takardar yabo kawai na samu daga Mataimakin Shugaban Kasa.

 

Kina ganin abin da mahaifinki ke yi ne ya hana a sabunta wa’adin aikinki?

E, da farko dai ma ba wani aiki ba ne idan aka yi la’akari da abin da wasikar aikin ta kunsa.

Da ma tun da muka ci zabe mahaifina ya ce min kar in kwallafa raina cewa sai an yi min wani abu, wataran zan samu.

Ya bayyana min cewa dukkanmu mun sadaukar a kanmu kuma wata rana zan ci ribar hakan in kuma kai matsayin da ya dace da ni.

Saboda haka ya ce kar in dauki samun mukami a matsayin makurar nasara ko in karaya saboda rashin ban samu ba.

 

Takwarorinki fa, ana biyan su?

E, galibinsu ana biyan su. Amman ba na nadamar yin aikin saboda yanzu ya shiga cikin bayanan kwarewata ta aiki.

 

Shin kin kai wa Mataimakin Shugaban Kasa korafi cewa ba a biyan ki?

E, ba ma sau daya ba. Yakan ba da umarnin a gyara matsalar amma da na bar ofis din shi ke nan ba za a yi ba.

Amma ba shi kadai ba ma, kowa ma ya sani.

 

A wata hira da aka yi da mahaifinki kwanakin baya ya ce ’ya’yansa bakwai ba su da aikin yi; shin ke ma kina daga cikinsu?

E, digiri bakwai gare ni amma ba ni da aiki. Na nemi aikin amma ba mai son ya ba ni.

A tunanina ni ba hadari ba ce amma wasu na mini kallon barazana, musamman saboda kasacewata mace Musulma mai ilimi kuma diyar Buba Galadima.

Ba ma aiki ba, ko kwangila na nema ba za a ba ni ba.

Ana nuna wa duniya cewa gwamnati ta rungume ni ta ba ni aiki. Har Festus Keyamo ya taba cewa wai na je wurinshi neman aiki, kawai saboda wasu sun yi masa karya shi kuma ya hau ya zauna ba tare da ya bincika ba.

Idan na ga dama zan kai shi kara saboda maganar tasa ba gaskiya ba ce.

 

Yaya alakar iyalan gidanku da iyalan Buhari take a yanzu da kuma kafin zaben 2015?

Matansu da ’ya’yan gidan aboka arzikin juna ne, to amma yanzu da suke gwamnati ba ma iya ziyartar su sai sun gayyace mu.

Amma mu abokan juna ne na sosai, duk iya dadewar da za su yi tabbas za su zo mu hadu. Haka kusancin yake.

Ina da kyakkyawar alaka da ’ya’yan gidan, ina zuwa gidajensu su ma suna zuwa gidana.

 

Kasancewar kin yi aiki a Fadar Shugaban Kasa, shin kina ganin Buhari ne ke da wuka da nama a gwamnatinsa?

Ba a Ofishin Shugaban Kasa na yi aiki ba, saboda haka ba zan sani ba.

Sannan ana gani na ne a matsayin diyar abokiyar gaba, a don haka ba ni da alfamar sanin yadda abubuwa suke tafiya, dole wani abin ba zan sani ba.

Amma mutane na gudanar da abubuwan da ke karkashin kulawarsu kuma na tabbata abubuwan da wasunsu ke yi bai sani ba.

Sukan dauki matakin da bai sani ba sannan ba na tunanin komai ne suke barin shi ya gudanar.

 

Kin taba haduwa da Shugaban Kasa a lokacin da kike aiki a fadar gwamnati?

A’a ban taba ba.

Akwai dai ranar da Shugaban Kasa ya hango ni daga nesa sai ya kwalla min kira, dukkanninsu sun cika da mamaki saboda bai saba yin hakan ba.

Ba wanda yake tsayawa ya yi magana da shi, amma ni ya tsaya yana tambaya ta yaya nake.

Ina ganin tun daga lokacin na fara shiga matsala – sai suke ganin cewa muddin aka bari na samu kusanci da shi to tauraronsu zai dishe.

Haka tunanin ’yan fada yake, kowanne kokari yake ya tadiye dan uwansa, da wuya ka samu mai taimakon ka. To ka ji yadda na fara shiga matsala.

 

Kina nufin kin fara shiga matsala a villa ne tun kafin mahaifinki ya fara sukar gwamnati?

Haka ne. Sun ga mahifaina ba ya cikin mukarraban gwamanti ga shi kuma a wurin babban taron jam’iyya yana yi wa Kwankwaso kamfen. Wannan ne zunubi a wurinsu.

 

A tunainki me ya sa mahaifinki ya bar Buhari ya koma goyon bayan Kwankwaso?

Ya goyi bayan Rabiu Kwankwaso ne ba don yana tunanin Buhari ba zai ci zabe ne.

Hasali ma ya yi ta bin hanyoyi daban-daban domin ba Buharin kwarin gwaiwar ya sake tsayawa takara amma ya ce ba zai sake tsayawa ba.

Shi ya sa mahaifina ya yanke shawara ya fara aiki tare da Kwankwaso kafin daga baya Buhari ya ce zai sake tsayawa takara, shi kuma mahaifina mutum ne mai amana.

 

Mutane na ganin mahaifinki ya goyi bayan takarar Shugaban Kasar Kwankwaso ne saboda a lokacin Kwankwaso gwamna ne, shi kuma Buhari shi da gwamnati a hannunshi.

Ba haka ba ne. Abin duniya bai taba jan ra’ayin mahaifina a kan duk matakin a zai dauka.

A wa’adin shugabancin Buhari na farko an ba shi manyan mukamai amma ya ki karba.

 

Shin kin taba ce wa mahaifinki ya daina caccakar Gwamantin Buhari?

E, na taba.

 

Wace amsa y aba ki?

Ce masa na yi yana jefa ni cikin hadari, amma sai ya ce ba zai daina ba saboda shi haka yake tun yana dan yaro.

 

Yaya kike ganin ayyukan gwamnati mai ci ta yi?

Ban jin dadin yadda ake samun rashin tuntuba tsakanin mutane da shugabanni; Ina ganin ya kamata su zauna tsakani da Allah su magance matsalolin.

Wasu mutanen fahimtarsu ta bambanta da saura game yadda za a kyautata abubuwa; irin wadannan mutanen kamata ya yi a sallame su.

Hakan na da matukar muhimmanci domin zai yi tasiri wajen alkalanci kan ko jam’iyyar APC za ta dawo sake cin zabe a 2023.

Akwai takaici yadda muka sadaukar da shekarunmu, hawayenmu da jininmu, wasunmu sun har mutuwa suka yi saboda wannan abu, amma har yanzu ba a share musu hawaye ba. Abin kunya ne.