Zazzafar muhawara ta barke a tsakanin ‘yan Najeriya game da dalilin tashin wuta a wani sashe na Ma’aikatar Kudi ta Tarayya da ke Abuja.
Wasu ‘yan Najeriya dai sun hau shafukansu na sadarwa suna zargin cewa da gangan aka tashi gobarar don cimma wata muguwar manufa.
- TNM za ta samar wa ‘yan Najeriya mafita a 2023 —Kawu Sumaila
- Bayan rahoton Aminiya iyalan ‘yan canjin da aka kama sun gana da mazajensu
Sai dai Ma’aikatar ta Kudi ta fitar da wata sanarwa a shafinta na Twitter tana musanta tashin gobara a ginin.
A maimakon haka, inji sanarwar, wasu batira ne da ke ajiye a wani dakin karkashin kasa suka kama wuta, kuma “nan take ma;aikatan tsaron da ke aiki a lokacin suka kashe wutar”.
Lamarin dai ya faru ne da sanyin safiyar Laraba, kuma ba da bata lokaci ba kafofoin sadarwa na zamani suka dauka, har ma wasu ‘yan Najeriya ke cewa watakila an cinna wutar ne da gangan, don boye wata almundahana.