Magoya bayan kungiyar Manchester United sun yi zanga-zanga a tsakiyar filin wasan Old Trafford domin nuna adawarsu ga iyalan Glazer, mamallaka kungiyar.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da United ke shirin karbar bakuncin Liverpool a ranar Lahadi inda za su yi haduwar gasar Firimiyar ta Ingila.
- Mayakan Boko Haram sun kashe Kwamandan soji a sansanin dakaru a Borno
- NCAA ta bai wa kamfanin Azman lamunin ci gaba da zirga-zirga
Haka kuma, an yi zanga-zanga a gaban Otel din da ’yan wasa da ma’aikatan United ke yada zango kafin karawar kungiyar da Liverpool.
Wannan lamari ya janyo aka dakatar da buga wasan duk da dai an bukaci magoya bayan da sauran jama’a su fice daga filin wasan.
Zanga-zangar dai ta samo asali ne tun yayin da kungiyar ta shiga cikin rukunin kungiyoyin da suka yi lale maraba da sabuwar gasar nan ta European Super League wacce ta janyo rabuwar kai a duniyar kwallon kafa.
Mahukunta kwallon kafa da sauran masu ruwa da tsaki ciki har da Hukumar kwallon kafar Turai (UEFA) da Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya FIFA sun juya wa gasar baya.
Tuni dai dukkanin kungiyoyi 6 masu buga gasar Firimiyar Ingila, suka janye aniyarsu ta shiga sabuwar gasar Super League ta Turai.
Manchester City ce ta fara ficewa bayan Chelsea ta nuna alamar janyewa daga cikin wannan gasa wacce ta kawo rudani a duniyar kwallon kafa.
Sauron kungiyoyin na Ingilia da suka janye aniyarsu bayan Manchester City da Chelsea sun hada da Arsenal, Liverpool, Manchester United da Tottenham.