A safiyar Juma’a jirage dauke da dalibai da sauran ’yan Najeriya da suka makale a Ukraine za su taso zuwa Najeriya, mako guda bayan barkewar yaki a Ukraine.
A ranar Alhamis jami’in da ke jagorantar kwaso ’yan Najeriya mazuana Ukraine da suka tsallaka zuwa makwabtan Ukraine, wadda yaki ya barke, Ambasda Bolaji Akinremi, ya sanar cewa ma’aikatan jiragen da gwamnati ta tura su kwaso su sun gaji, don haka aka dage dawowar.
- NAJERIYA A YAU: Dalilin Watsi Da Dokar Ba Mata 35% na mukaman shugabanci
- Farashin man fetur ya yi tsadar da bai taba yi ba cikin shekara 10
“Gaskiyar magana ita ce an dage lokacin tashin jiragen da za su kwaso su zuwa goba (juma’a) da safe,” kamar yadda ya sanar a kasar Poland.
Da farko Gwamnatin Tarayya ta ce rukunin farko na ’yan Najeriya 2,090 mazauna Ukraine da za a kwaso daga kasashen Poland, Romania da Hungary da sauran kasahen Gabashin Turai za su fara isowa Najeriya ne a ranar Alhamis.
Ana cikin jiran saukar jiragen da gwamnatin ta tura domin kwaso su a filin jirgi na Nnamadi Azikiwe da ke Abuja, sai ga sanarwar dage dawowar tasu zuwa Juma’a.
Musabbabin dage lokacin
Ambasda Bolaji Akinremi, ya bayyana cewa an tasowar jiragen da za su kwaso su zuwa ranar Juma’a ne saboda ma’aikatan jiragen su sun yi aiki fiye da ka’idar aikinsu.
“Babban dalilin dagewar shi ne jinkirin da aka samu wajen tattarowa da tantance fasinjojin saboda daga otal-otal a wurare daban-daban aka kwaso su, kafin a gama ma’aikatan jiragen da ke jira tun karfe 9 na safe sun wuce ka’idar lokacin jira da tashi a bisa ka’idar aikinsu.
“A ka’idar lokacin da aka kayyade na jira: Sun yi awa biyar suna jira, tun karfe 9 na safiya zuwa 2 na rana, ga shi tafiyar ta awa tara ce, wanda hakan ya saba ka’ida; Shi ne mahukunta filin jirgin suka hana mu tashi,” kamar yadda jami’in ya bayyana a Poland.
Ambasda Akinremi ya bayyana a ranar Alhamis din cewa zuwa lokacin, duk ’yan Najeriyan da za a kwaso daga Poland an tara su a otal daya, kuma za su baro kasar ranar Juma’a.
A nasa bayanin, Jakadan Najeriya a Poland, Christian Ugwu, ya ce an yi jan aiki wajen tattaro ’yan Najeriyan da ke kasar a wuri guda, yana mai ba da tabbacin cewa a ranar Juma’a za su baro kasar.
Akalla ’yan Najeriya 2,090 ne za a kwaso daga kasashen Poland, Hungary, Romania da sauran kasashen Gabashin Turai a sakamakon barkewar yakin da Rasha ta kaddmar a Ukraine, mako guda da ya wuce.