Cibiyar nazarin zaman lafiya da ke Stockholm (SIPRI) ta ce za a samu karuwar makaman nukiliya a duniya saboda tashe-tashen hankula da suka mamaye ko’ina.
Duk da cewar an samu raguwar adadin makaman nukiliya zuwa kimanin 12,705 a fadin duniya, a rahotanta na shekara-shekara da aka wallafa a ranar Litinin, cibiyar ta ce tabbas wannan adadin zai karu cikin shekaru goma masu zuwa.
- Jiga-jigan tsohuwar jami’yyar CPC na son Malami ya zama abokin takarar Tinubu
- Makiya ke ruruta wutar zanga-zanga a Iran —Khamenei
Kwararre a cibiyar, Hans Kristensen ya bayyana cewa, alamun raguwar makaman nukiliya tun bayan da aka kawo karshen yakin cacar baka ya zo karshe, kuma idan kasashen da ke mallakar makaman nukiya ba su dauki matakai ba, akwai yiwuwar habakarsu fiye da yadda ake a yanzu.
Rahoton na SIPRI na nuni da cewa har yanzu Rasha da Amurka ne ke mallakar kaso 90 na makaman nukiliyar da duniya ke da su, inda Rasha ke mallakar 5,977 kana Amurka ke da 5,428.
Dalilin da muke kera makamin kare dangi —China
Gwamnatin China ta sanar da cewa ta yi nisa wurin kera makamin nukiliya domin tsare martabarta a idon duniya.
Ministan Tsaron Kasar, Wei Fenghe, ne ya sanar da haka a ranar Lahadi a yayin taron koli kan harkokin tsaron yankin Asiya da ke gudana a Singapore.
Ministan ya ce shekaru sama da 50 suka kwashe suna kokarin kera makamin.
Tun a shekarar da ta gabata Amurka ta ce ta bankado yadda China ke bunkasa makamashin nukiliya ba tare da sanin duniya ba.
To sai dai ministan tsaron Chinan ya ce burin kasarsa shi ne kokari na dakatar da amfani da makamin kare dangi a duniya ta hanyar kare martabarta.
Mahukunta a Chinan sun ce za su yi amfani da makamin nukiliyar ne kawai a wurin kare kansu, kuma ba za su taba fara amfani da makamin ba, sai idan wani ya fara kawo musu hari da shi.