✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dalilin da ’yan majalisar Birtaniya ke tsoron shiga jama’a

Hakan na zuwa ne bayan kisan wani dan majalisar da aka yi a ranar Juma’a.

’Yan majalisar Birtaniya sun fara tuntubar juna dangane da barazanar rasa rayukansu da suke fuskanta a yayin da suka shiga jama’a wajen sauke nauyin da rataya a wuyansu.

Kafofin watsa labarai na kasar sun ruwaito cewa, ’yan majalisar sun shiga tuntuba tare da bai wa junansu labarin gami da alhinin wannan kalubale da suke fuskanta a zaurukan sada zumunta musamman mahajar WhatsApp.

Da dama daga cikinsu sun fara tunanin yanke shawarar ficewa daga mazabunsu tare da iyalansu tare da nufin sauya wuraren zama domin gudun abin da ka iya zuwa ya dawo.

Sir Charles Walker, daya daga cikin ’yan Majalisar Wakilai wato House of Commons, ya bayyana damuwa gaya dangane da yadda abokanan aikinsa ke bayar da rahoton fuskantar barazana ta rasa rayuwa ko cin zarafi.

A kan hakan ne ’yan majalisar a ranar Litinin za su yi zama na musamman domin yi wa wannan lamari na matsalar tsaro da suke fuskanta tufka.

Duk wannan dai na zuwa ne bayan kisan wani dan majalisar Birtaniya, Sir David Amess da aka yi a ranar Juma’ar da ta gabata.

Rahotanni sun tabbatar da cewa, wani matashi dauke da wuka ne ya hallaka dan majalisar na jam’iyyar Conservative ta Firaminista Boris Johnson.

Matashin dan shekaru 25 ne ya kai hari kan dan majalisar mai shekaru 69 lokacin da yake ganawa da ’yan mazabarsa a Majami’ar Methodist da ke gabashin Ingila.

Tuni dai ’yan sanda sun tabbatar da kama maharin, wanda suka ce shi kadai ne ya aikata wannan danyen aiki, wanda suka ce hari ne na ta’addanci.

Wannan lamari da na zuwa a daidai lokacin da ’yan majalisar dokokin ke matsa kaimi wajen tsaurara matakan tsaro bayan kisan wanda ke zama ’yan siyasar Birtaniya na biyu da ke mutuwa yayin da suka ganawa da al’ummar mazabunsu cikin shekara biyar.

A shekarar 2016 ce aka kashe wata ’yar majalisar mai suna Jo Cox a yayin da take ganawa da jama’ar mazabarta ta Yorkshire a yawon yakin zaben tabbatar da kasancewar Birtaniya a cikin kungiyar Tarayyar Turai ta EU.

%d bloggers like this: