✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin da ya sa Shata ya yi mini waka – Ummaru danduna na Gwandu

Alhaji Umaru danduna Na-Gwandu, mutum ne da ya shahara a harkar tukin mota, kuma wakar da Dokta alhaji Mamman Shata Katsina ya yi masa, ta…

Alhaji Umaru danduna Na-Gwandu, mutum ne da ya shahara a harkar tukin mota, kuma wakar da Dokta alhaji Mamman Shata Katsina ya yi masa, ta kara tallata shi a duniya.  Don haka Aminiya ta garzaya gidansa da ke Kano don tattaunawa da shi kan dangantakarsa da Shata da kuma halin da ya tsinci kansa a rayuwar yanzu, wadda ta saba da ta da. A cikin hirar ya yi bayanin dalilin da ya sanya Shata ya yi masa waka, ga dai yadda hirar ta kasance:
Aminiya: Ko za ka yi bayanin rayuwarka a takaice?
Alhaji Umaru: A’uzu billahi minas shaydanir Rajim, Bismillahir Rahamanir Rahim. Godiya ta tabbata ga Allah da kuma gidan jaridar Aminiya da suka ziyarce ni don jin labarina. Ni dai ina jin cewa ina da shekara 85  a duniya, kodayake na dan rage. Kuma tun da na taso babu abin da na sani sai harkar mota. Na yi tuki a kasashen Afirka ta Yamma, musamman tsakanin Najeriya da Nijar.
Aminiya: Alhaji ba ka bayyana mana yawan iyalinka ba, musamman ma jin cewa shata ya ambaci sunan matarka Jamma, wadda kuka tafi Nijar da ita?
Alhaji Ummaru:: E, haka ne. Na haifi ’ya’ya 16, tsakanin matattu da rayayyu; kuma jikoki ina da 47
Aminiya: Ko za ka gaya mana abokan gwagwarmayarka a harkar tukin mota?
Alhaji Ummaru: Ka san ita mota tana da iyaye da ’ya’ya da jikoki, amma wanda zan iya cewa shi ne babana na tuki, dahe Na-Nana, sai kuma Ubangidana wanda ya koya mini tuki, danduna Na-Mushe. A abokai kuwa, akwai Sarki Labaran da Musa Bellon Laure da Sani Sagir. Mafi yawan iyayen gidana da abokan tukina duk sun rasu, muma ba mu san hikimar da ta sa Allah Ya barmu ba. Wannan dai nufi ne naSa.
Aminiya: Alhaji Ga shi ka shahara saboda wakar da shata ya yi maka, kusan duniya ta ji sunanka, wacce irin dangantaka ke tsakaninka da wannan mawaki?
Alhaji Ummaru: Dokta Alhaji Mamman Shata abokin danduna Na-Mushe ne, wanda kuma shi ne maigidana, shi ya koya mini mota. Kuma shi dandunan nan, duk abin da Uba ke yi wa da ya yi mini, ni ma duk irin biyayya da da yake yi wa mahaifinsa, ni ma na yi masa; sai dai ina ganin ban biya shi ba. Kai shi kansa Alhaji Mamman Shata ya dauka danduna ne ya haife ni, amma ni mutumin Gwandu ne, ta Jihar Kebbi, shi kuwa mutumin Maiduguri ne. Ganin yadda nike bin danduna da girma da mutunci, shi ma Shata sai ya rike ni da mutunci. Don haka har yau ina yi musu addu’a Allah Ya sanya aljanna ce makomarsu. Amin.
Aminiya: Wato dai kuna da kyakkyawar dangantaka da Shata?
Alhaji Ummaru: E, ka san shi Mamman Shata kauna ta hakika ce tsakanina da shi. Domin da ya ga babu danduna Na-Mushe, sai ya mayar da ni matsayinsa. Ni kuwa duk abin da danduna ke yi wa Shata na kan yi gwagwardon iyawata, wani abun ma tun ba ni iyawa, har na kai ga ina iyawa. Direbobi suka yi ta yi mini dariya, suna yi mini tsiya suna cewa wai Shata ya yi wa kowa waka amma ban da ni, ga shi kana cewa Shata babanka ne. Wata rana sai Shata ya kira ni, ya ce ka yi hakuri, ina rokon Allah ya ba ni dama in fadi wani abu a kanka, ta yadda duk mai tuka mota a Afirka ta Yamma sai ya san da kai. Kai ina so in fita kunyar danduna Na-Mushe, domin da zai dawo duniya ya ji ban ce komai game da kai ba, ai abin da kunya. Wata rana sai Kamfanin daukar wakoki a faifan garmaho ya gayyaci Shata Legas, don ya yi musu waka su dauka, yana zuwa kuwa wakata ya fara yi. Da fitowarsa, sai ya ganni na yi lodi zan tafi, sai ya zo ya kama hannuna, sai ya ce a sanya wakata. Wannan waka dai ta tabbata kamar wasa, amma duk abin da ya fada sai da ya tabbata. Don haka masoyana suka cika da farin ciki, su kuma makiya sai suka cika da bakin ciki.
Aminiya: Wacce daukaka wakar  Shata ta haifar maka?
Alhaji Ummaru: Na gaya maka danduna ya koya mini mota, Shata kuma ya tallata ni a duniya. Na kuma rabu da mota lafiya, domin babu shari’a, babu hadari. Ina kuma yi wa sauran direbobi ’ya’yana da jikoki addu’a Allah Ya raba su da karfe lafiya, amma su guji shan kwayoyi da kayan maye. Sannan ina gargadinsu da su rike amana, domin duk wanda ya ba ka mota dukiyarsa ya sanya ya saya. Ka ga mu a lokacinmu bilhakki muka yi aiki, shi ya sa Allah Ya raba mu da ita lafiya.
Aminiya: Alhaji ga shi kana fama da laulayi, wacce irin larura kake fama da ita?
Alhaji Ummaru: Rashin lafiya tashi yake, amma laulayi girma ne da wahala irin ta da.
Aminiya: Ko akwai wadanda ke taimakawa wajen dawainiya da kai, a irin wannan hali da ka samu kanka?
Alhaji Ummaru: E, akwai wadansu iyayen gidana, wadanda ba su da gefe, kuma su ne Mai girma Galadiman Kano Alhaji Tijjani Hashim da dansa Alhaji Bello Isa Bayero, wato a sarakai ke nan. A ’yan Kasuwa kuwa akwai Alhaji Aminu Baba danBappa; a ’yan siyasa kuwa ba ni da sama da Janar Muhammadu Buhari, kodayake  dan Majalisar Nasiru Ahmad Ali shi ma ya yi rawar gani. A halin gaskiya ba ni da sama da Alhaji Mustapha Ammasco, tunda ya taba sanyawa aka dauko ni aka yi hira da ni ta awa hudu, aka sanya tallar kamfanin man sa da ni, sannan ya kawo alheri mai yawa ya yi mini. A gaskiya da zan samu irin Ammasco biyu, ai shi ke nan na warke.
Aminiya: Shin wadannan mutanen ko sun san ba ka da lafiya?
Alhaji Ummaru: Ta yiwu sun sani, wasu kuwa ba su sani ba.