Naziru M Ahmad fitaccen mawakin Hausa ne, a hirarsa da Aminiya a lokacin daukar albam din ‘Kukan Kurciya’ na Adam A. Zango a Kaduna kwanakin baya, ya bayyana yadda ya fara waka, sannan ya yi karin haske kan butun da ake cewa zai auri jaruma Hadiza Gabon.
Za mu fara da tarihinka a takaice?
Assalamu alaikum, sunana Nazir Muhammad Ahmad. An haife ni a unguwar Gwammaja da ke birnin Kano a shekarar 1986. Na fara karatun addini a gidanmu a shekarar 1992, na yi karatu a makarantar Nurul Dhalal. Na kuma wuce Kwalejin Darussan al-kur’ani wato (College of kur’anic Studies), daga nan na koma makarantar Kings College da ke unguwar Rijiyar Lemo, inda na kammala a shekarar 2010.
Tun yaushe ka fara harkar waka, kuma me ya ja hankalinka har ka fara waka?
Sha’awa ce ta sa na fara waka, saboda kowa Allah Ka iya sanya masa kaunar wani abu a zuciyarsa. Na kuma fara ne a shekara ta 2000, inda na yi wata waka mai suna ‘Caryaryar’ ta cikin fim din ‘Musnadi’.
Me ya sa wadansu lokuta kake daukar salon wakokin gargajiya?
Saboda wakokin gargajiya muka gada daga iyaye da kakanni. Yana da kyawu a fahimci ba kawai salon wakar ne na gargajiya ba, hatta kayan kidan da muke amfani da su a wasu wakokina na gargajiya ne. Irin salon zamani da aka saba gani, salo ne da muka aro daga wasu. Ka san masu iya magana na cewa kowa ya bar gida, gida ya bar shi, kuma kowane tsuntsu kukan gidansu ya kamata ya rika yi.
Zuwa yanzu ka yi wakoki nawa?
Akalla za su kai dari, ba ni da wata bakandamiya a cikinsu. Kowacce a cikinsu ina ji da ita, kuma bakandamiya ce.
Ko za ka yi wa masu karatu karin haske kan wakar ‘Garin da Ake Kurba Man Gyada Zalla’ ta cikin fim din ‘Wani Gari’ da kuma ‘Da Kudin Ku Kuke ta Saya’
Da farko wakar ‘Garin da Ake Kurba Man Gyada Zalla’ ga wadanda suka kalli fim din, wani mutum ne da ya tara dimbin dukiya, amma ba shi da ilimi, ba ya ba da zakkah da taimako da sauransu. Kamar yadda aka gani a fim din, masu irin wannan hali dukiyarsu ce kan kai su ga halaka.
Har ila yau, dalilin yin wakar ‘Da Kudin Ku Kuke ta Saya’ shi ne, kalubalen da mu mawakan Hausa muke fuskanta daga wasu daga cikin masu sauraron mu. Misali za ka ga wasu sun fi so su ga ’ya’yansu sun tasiransu da rayuwa irin ta nasara. Za ka ga irin wadannan mutanen su ne, masu sukar mu ko da kuwa sun fahimci wakokinmu sako suke isarwa, ba batsa ba. Amma da za su ji ’ya’yansu na yin wakokin Turawa wadanda wasu ma kalaman batsa suke dauke da su, ba sa tsawatar musu ko kuma ka ji sun soke su. Masu wannan tunanin sun fi so jama’armu su mika kudin mu ketare, madadin su kashe su a gida.
Me ya sa kake zabar mutanen da kake yi wa waka?
Da farko ina yin wakokin ne na ajiye, kodayake daga bisani idan wani ya saurara kuma ya ji yana bukatar ya yi amfani da ita a fim, sai ya zo ya same mu. Idan muka duba muka ga fim din da zai sa wakar mai ma’ana ne sai mu ba shi izini.
Tun bayan da Hadiza Gabon ta fito a wakokin albam dinka aka rika watsa jita-jitar akwai soyayya mai karfi a tsakaninku, har an fara batun za ku yi aure, me za ka ce kan hakan?
Ba gaskiya ba ne. Babu batun soyayya a tsakanina da ita.
Yaya batun dangantaka ta jini tsakaninka da mawaki Misbahu M. Ahmad da kuma Darakta Aminu Saira?
Dukkansu yayyena ne uwa daya, uba daya.
A yawancin wakokinka kakan yawaita koda kanka, ko me ya jawo hakan?
A waka daya kawai na taba koda kaina, kuma wasu nake tsokana wadanda ma ba su danganci wakar ba. Saboda idan ina waka kuma wani ya shigo dakin da ake daukar wakar nakan hada da shi. Misali idan ina waka a kan maza, sai wata mace ta shigo, to zan iya sanya ta a ciki. Domin ba rubuta waka nake yi ba, ina kirkirar ta ne a lokacin da za mu yi ta. Kodayake mukan zauna mu kirkiri kidan waka kafin fara daukarta.
Me ya sa aka yi maka lakabin ‘Mai Waka’?
Ana kira na haka ne saboda wata waka da na yi mai suna ‘Mai Waka’.
Me ya sa ba ka fitowa a fina-finai?
Saboda ba na sha’awa. Amma akwai wasu da ke cewa ina fitowa a fim. A gaskiya ba ni ba ne. Abin da ke faruwa shi ne, rashin iya bambanta fuskata da ta yayana Misbahu M. Ahmad, wanda yake mawaki kuma jarumi da ke fitowa a fina-finai.
A yanzu wane kalubale kake fuskanta?
Ina fuskantar babban kalubale. Tun da ita kanta harkar har yanzu ba ta zauna da gindinta ba.
Wane buri kake so ka cim ma a harkar waka?
Babban burina shi ne mu ga harkar nan ta daidaita da fadin malamai da addini. Babban burina in raba wannan harkar da duk abin da ba addini ba ne.
Ko akwai wadansu harkokin da nake yi bayan waka?
Ina da kamfanin aikin gine-gine, sannan ina harkar sayar da motoci, a yanzu muna kokarin gina wani gidan gona. Amma fa mun fi karfi a sana’ar waka, saboda ita ce sila kuma ta fi bukatar lokaci sosai.
’Yan siyasa da yawa sun nemi ka yi musu waka amma ka ki, ko me ya jawo hakan?
A gaskiya ina yi wa ’yan siyasa waka, amma fa ba kowane ba. Nakan fara auna duk dan siyasar da zan yi wa waka ta hanyar la’akari da irin dabi’unsa da kuma dangantakarsa da jama’a, saboda idan ba shi da amfani ga jama’arsa, ba shi da amfani a wajena, ko da kuwa nawa ya mallaka.
Batun iyali fa?
Ina da mata biyu da ’ya’ya biyu.