✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin da ya sa na bude gidan abinci- Fati Bararoji

Shahararriyar jarumar fina-finan Hausa Fati Baffa Fagge da ake yi wa lakabin Fati Bararoji ta ce ta bude gidan abinci mai suna Fati Bararoji Restaurant…

Shahararriyar jarumar fina-finan Hausa Fati Baffa Fagge da ake yi wa lakabin Fati Bararoji ta ce ta bude gidan abinci mai suna Fati Bararoji Restaurant don ta raba kafa, don kuma ta samar da abinci mai gamsarwa da dandano.
Ta ce: “Bai kamata mutum ya tsaya a kan abu daya ba kawai, yana da kyawu ya raba kafa, ba ka ji an ce gida biyu maganin gobara ba? Na san harkar fim, ina da wadansu harkokin kasuwanci kuma, amma duk da haka mutum ba zai daina nema ba, tun da idan ba ka da shi babu wanda zai ba ka, baya ga haka ina da sukunin hada harkar fim da kasuwancina da kuma wannan gidan abincin da na bude.”
Ta nemi jama’a su yi mata addu’ar Allah Ya sanya wa gidan abincin nata albarka.
Gidan abincin da ke kan Titin Zoo Road kusa da Bankin Union a Birnin Kano an yi bikin bude shi ne a kwanakin baya, inda ’yan fim da ’yan uwa da abokan arziki suka taru, aka ci, aka sha, sannan aka yi mata addu’a.