✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin da ya sa muka yi sabon shugaba a Gombe – Muryar Talaka

kungiyar Muryar Talaka ta kasa ta tunbuke Shugaban kungiyar na Jihar Gombe, Kwamared Affan Buba Abuya ta maye gurbinsa da sabon shugaba, biyo bayan takaddamar…

kungiyar Muryar Talaka ta kasa ta tunbuke Shugaban kungiyar na Jihar Gombe, Kwamared Affan Buba Abuya ta maye gurbinsa da sabon shugaba, biyo bayan takaddamar da ta kunno kai a a yayin gudanar da babban taronta a Gusau na Jihar Zamfara a farkon watan jiya, inda aka fara samun rabuwar kai game da matakin da uwar kungiyar ta dauka na yin karin wa’adi ga shugabannin kungiyar karkashin jagorancin Zaidu Bala Kofa Sabuwa.

Aminiya ta ruwaito yadda aka toya wainar a wancan karon, inda shugabannin jihohin Gombe da Jigawa suka ki amincewa da sakamakon da uwar kungiyar ta fitar game da tsawaita wa’adin shugabannin, sannan suka fice a zaure taron, kana kuma suka kira taron da suka kira na dinke baraka a kungiyar wanda ya gudana a Kano a makon jiya.

Sabon shugaban rikon shi ne Adamu Babale Makera, kamar yadda Babban sakaren kungiyar na kasa, Kwamared Bishir Dauda ya shaidawa wakilinmu. “Alhamdulillahi, tunda yanzu uwar kungiya ta kasa, karkashin jagorancin mai girma shugabanmu Zaidu Bala Kofa Sabuwa Birnin Kebbi, ta dauki matakin da tuntuni ya kamata a ce ta dauka akan tsohon shugaban kungiyar a nan jihar Gombe, kuma madugun tawaye, yanzu za a bude sabon babi a tarihin wannan kungiya a jihar Gombe,” in ji shi.

A yayin da yake maida jawabin, jim kadan bayan nada shi shugaban rikon, Adamu Babale Makera ya godewa uwar kungiyar bisa matakin da ta dauke, sannan ya bukaci mambobin kungiyar a jihar Gombe sub a shi hadin kai don ciyar da ita gaba. 

“Hakika ba zamu bari a rika yi wa wannan kungiyar kallon matattarar marasa da’a, masu zagin shugabanni da zage-zage a tsakaninsu ta kafafen yada labarai da shafukan sada zumunta na Intanet ba. Rashin da’ar da tsohon shugaban ya je ya yi a babban taron kungiyar da akai a Gusau kwanakin baya, mu bada yawunmu ba. Domin bai tuntubi kowa ba, hasali ma shi kadai ya halarci taron, saboda da ma ya yi kokarin ya tunzura mutane su ki halartar taron, to amma hakarsa ba ta cimma ruwa ba. Domin kungiyar a Jihar Gombe karkashin shugabancina ba za ta lamunci zagin shugabanni da iyayen kungiya ba.” Ya karkare.