✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin da ya sa mayankar Abuja ke cikin mummunan yanayi – FCDA

Babbar Daraktar Al’amuran Dabbobi a Sakatariyar Noma ta Ma’aikatar Birnin Tarayya (FCDA), Abuja, Dokta Regina Adulugba ta ce manyan mayaka hudu da suke karkashin ma’aikatar…

Babbar Daraktar Al’amuran Dabbobi a Sakatariyar Noma ta Ma’aikatar Birnin Tarayya (FCDA), Abuja, Dokta Regina Adulugba ta ce manyan mayaka hudu da suke karkashin ma’aikatar suna fama da cinkoson da ya zarce yadda aka tsara su ne sakamakon karuwar jama’a da birnin ya rika samu bayan gina su kimanin shekara 30 da suka gabata.

Daraktar wadda ta yi magana a madadin Sakataren Riko na Sakatariyar, Dokta Musa Aliyu  ta yi korafin cewa gwamnatocin da suka gabata sun gaza aiwatar da gyare-gyaren yau da kullum da wuraren suke bukata duk shekara, in ban da na garin Karu da Ma’aikatar Gona ta Tarayya ta aiwatar a baya. 

Daraktar tana mayar da jawabi ne kan binciken da Aminiya ta yi game da mummunan yanayin da mayakar Abuja suke ciki, inda ta ce Ministan Birnin Tarayya, Malam Muhammad Musa Bello ya sanya batun yi wa mayakan gyara a kasafin kudin bana, kuma ta ce da zarar kasafin ya samu amincewa za a kaddamar aikin gyara mayakar hudu da ya hada da samar musu da ruwa da daga katangar da suka rushe da farfado da kananan magudanun ruwa da suke daukar jini da ruwa zuwa inda ya dace da su.

A cewar Daraktar, tattaunawa a tsakanin sakatariyarsu da Ma’aikatar Gona ta Tarayya ta yi nisa a kan yadda za a samar wa mayakar hudu motocin dakon nama don jigilarsa zuwa kasuwanni. Kuma ta ce Ministan ya amince da daukar sababbin likitocin dabbobi 20 da karin jami’ai 13 a sashin don inganta aiki a mayakar hudu da sauran wurare. 

Dokta Adulugba wadda ta yi Allah wadai da yin gine-gine a cikin wasu fulotan mayakar, inda ta bayyana hakan da wani abu da ya faru a baya da ba ta da cikakken masaniya a kai, ta ce a kokarin da suke yi wajen rage cinkoso a mayankar da kuma tsabtace su, sun rushe bacoci da kawar da wasu sana’o’i da ba na fawa ba a harabobin mayankar Karu da Kubwa kwanakin baya.

Ta ce baya ga manyan mayaka hudu da wata mai zaman kanta a garin Deidei da ke karkashin kularsu kai-tsaye, ta ce ragowar mayankar Abuja suna karkashin kananan hukumomin yankin ne saboda su ne suka gina su kuma su ke sa ido a kansu, saboda haka ta ce ba su da masaniya a kan abubuwan da suke faruwa a wuraren duk da cewa sakatariyarsu ce ke tsara wa hukumominsu dokoki.

“Sai dai ina son in bai wa mazauna Abuja tabbacin cewa Ministan Birnin ya ba mu damar gina sababbin mayanka na zamani guda 6 ta tsarin hadin gwiwa a tsakanin gwamnati da ’yan kasuwa (PPP) a garuruwan Karshi da Lugbe da Dutsen-Alhaji da Bwari da kan hanyar filin jiragen sama na Abuja,” inji Daraktar.