Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta ce da zarar wa’adin da ta sa na ranar 31 ga watan Yulin 2022 domin kammala rajistar masu zabe ya cika, ko kwana daya ba za ta sake karawa ba.
Kwamishinan Hukumar mai kula da bangaren wayar da kan masu zabe, Festus Okoye ne ya bayyana hakan a Awka, babban birnin jihar Anambra, yayin zantawarsa da ’yan jarida a ranar Asabar.
- JIBWIS ta tara miliyan 100 daga fatun layyar da aka ba ta — Sheikh Bala Lau
- Tikitin Musulmi da Musulmi ya gwara kan Tinubu da Atiku
Ya ce za a rufe yin rajistar ce domin hukumar ta sami damar ci gaba da sauran shirye-shiryen babban zaben 2023 da ke tafe.
A cewar Festus, da zarar wa’adin ya cika, hukumar za ta fara aikin tantance rajistar domin gano wadanda suka yi fiye da sau daya da kuma aikin buga katinan zaben.
Kwamishinan ya kuma ce wadanda suka yi rajistar da kuma wadanda suka sabunta ta daga tsakanin watan Janairu zuwan Yunin 2022, za su karbi katinansu a watan Oktoba mai zuwa.
Sai dai ya ce mutanen da suka yi rajistar a watan Yuli kuwa za su jira sai a watan Nuwamba mai zuwa kafin su fara karbar katinan nasu.
Da yake amsa tambaya a kan irin shirin da INEC ta yi wa zaben na 2023 kuwa, Festus Okoye ya ce a shirye suke su gudanar da sahihi kuma ingantaccen zabe da jama’a za su amince da shi.