✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin da Shata ya yi mini waka -Hamza dan Labaran

Ya Alhaji Hamza dan LabaranA sha iska a koma gariYanzu aikin uba nai yakeIn ba ya garinsu ya kwan biyuHamza am! Ya tai kasashen waje…

Ya Alhaji Hamza dan Labaran
A sha iska a koma gari
Yanzu aikin uba nai yake
In ba ya garinsu ya kwan biyu
Hamza am! Ya tai kasashen waje

Alhaji Hamza dan Labaran, tsohon malamin makaranta ne, dan kasuwa, kuma tsohon dan siyasa wanda ya shahara a wakar Shata, mai taken “Ya Alhaji Hamza dan Labaran.” Aminiya ta tattauna da shi kan al’amuran da suka shafi tarihin rayuwarsa da yadda aka yi har Shata ya yi masa waka. Ga dai yadda hirar ta kasance:

Aminiya: Alhaji ko za ka bayyana mana tarihin rayuwarka?
Alhaji Hamza: An haife ni a shekarar 1940, na yi makarantar allo a makarantar Malam Abba da Malam Babale a Alfindiki. Daga nan na shiga Shahuci Judicial, wadda a halin yanzu aka fi sani da  makarantar Aliya. Bayan shekara biyu, sai na halarci Babbar Firamaren Birni ta “City Senior Primary School,’ wadda a halin yanzu an mayar da ita makarantar ’yan mata da ke Shekara a hanyar zuwa kasuwar Rimi cikin birnin Kano. Na shiga wannan makaranta a shekarar 1957, inda na shafe shekara uku, wato zuwa 1959; a wancan zamanin ta kwana ce (boarding). Daga nan sai aka kai mu wata makaranta da ake kai wadanda ba su samu shiga Sakandare ba wato Post Primary School da ke Gwarzo, inda muka yi ta karatu tun daga 1959 har zuwa 1961. Sannan na halarci Kwalejin Horon Malamai ta Kano (KTC). Bayan na samu nasarar cin jarabawar kwarewa a koyarwa mai daraja ta biyu (grade II), sai na fara koyarwa a Makarantar Firamare ta Madatai.
Aminiya: Ko ka yi wadansu aikace-aikace na hukuma?
Alhaji Hamza: A’a. Na bar koyarwa na tafi Landan karatu, amma ban dade ba, sai Allah Ya yi wa mahaifina rasuwa. Sai na dawo a wajen shekarar 1968, na ci gaba da harkokin kasuwancinsa na safara zuwa kasashen Afirka, wadanda suka hada da Kongo da Ghana, inda na yi ta zuwa ina dawowa kan harkar saye da sayarwa. Baya ga aikin koyarwa ban yi aikin gwamnati ba, sai dai siyasa.
Aminiya: Ko za ka bayyana irin rawar da ka taka a fagen siyasa?
Alhaji Hamza: A zamanin Gwamna Rimi na yi jam’iyyar PRP, inda na zama Kansilan kudi da na ayyuka. Kuma daga bisani Shugaban karamar Hukumar Birni da Kewaye (Kano Municpal) ya samu rashin jituwa da Gwmanatin Rimi, don haka aka cire shi aka nada ni, amma ni ma ban wuce tsakanin shekarun 1981 zuwa 1982 ba, aka cire ni.
Aminiya: Yaya ka ci gaba da gudanar da harkokin rayuwa a lokacin mulkin soja?
Alhaji Hamza: Babu abin da na yi daga kasuwanci sai ’yan bige-bige.
Aminiya: A ina kuka hadu da Alhaji Mamman Shata har ya yi maka waka?
Alhaji Hamza: Ina kyautata zaton an yi wakar a tsakanin 1968 zuwa 1969, domin a lokacin na dawo daga Landan, bayan rasuwar mahaifina. Na kuma daina karatun da nike yi a can saboda wasu dalilai. Wata rana su Sarki Labaran suka gayyace ni kallon wasa, sai kawai Shata ya yi mini waka. Kuma idan ka je ka tambaye su, Sarki Labaran da Umaru danduna duk sun fi ni sanin komai game da Alhaji Mamman Shata. Ni, a halin yanzu, ba ni iya tuna wasu abubuwa saboda larurorin da na samu a baya. Ka ga yanzu kafata ba ta iya tsayawa, sai an rike ni, ko kuma da sanda.
Aminiya: Wacce irin kyauta ka yi wa Shata ta burge shi, har ya yi maka waka?
Alhaji Hamza: Kyauta ka san dole a yi ta, amma ni ba ni iya tuna kyautar da na yi wa Shata ta burge shi. Na san dai na yi masa kyauta.
Aminiya: A cikin mawakan Hausa na wannan zamanin ko kana ganin akwi mai basir airin ta Shata?
Alhaji Hamza: A ina za a samu? Ai ba na ji akwai wani mawaki kamarsa a yanzu. Sai dai baiwar Allah.