Jihar Sakkwato an san ta sosai ga kiwon awaki a Afirka ta Yamma gaba daya, ba a Najeriya kadai ba. Da wuya ka samu gidan da ba a kiwon akuya, musamman kauyukan jihar.
Hakan ya sa a kasuwar sayar da dabbobi da ake kira Kara, a kowace ranar Juma’a ko Litinin ana shigo da awaki kusan 5000 daga kananan hukumomi 23 na jihar, ana sayar da su ga makawabtan jihohi da kasar Nijar da sauransu.
- Abin tsoro dangane da daminar bana
- An kashe malamin addini da manoma 5, an sace mutum 40 a Birnin Gwari
Akuya ta fi saukin kudi a cikin dukkan dabbobi masu kafa hudu. Da Naira dubu hudu za ka samu mai girma da ake iya yin duk wani abu da ake so a Kasuwar Kara.
Binciken Aminiya ya gano cewa mutane da dama a Jihar Sakkwato ba su cin naman akuya saboda wani dalili na kashin kansu ko kuma wata al’ada da ta shafi gidansu ko danginsu da kabilarsu.
Shehin Malami a fannin ilimin tarihi a Jami’ar Usman Dan Fodiyo, Farfesa Mukhtar Umar Bunza ya ce wannan lamari an yi tsawon shekaru ana yin sa amma yanzu an samu raguwar lamarin, ganin yadda Kungiyar Izala ta yi tasiri wajen fadakar da mutane abin da shari’a ta amince da shi.
A cewarsa, a lokacin baya shi da kansa ba ya cin naman akuya saboda yana ganin kamar in ya ci naman zai rika yin halayya da dabi’a irin nata.
“Kada ka mance, akuya a kowane lokaci tana kuka da damun mutane, sai nake ganin kamar idan na ci namanta zan yi abin da take yi,” inji shi.
Wani dalili kuma ya ce, wanda ya kafa Daular Sakkwato Sheikh Usman Danfn Fodiyo ba ya cin naman akuya. Kan haka ya sanya wadansu ba su ci, musamman Fulanin da aka kira Torankawa.
“Karantarwar Izala kan bin karantarwar Annabi Muhammad (SAW) da sanar da jama’a dukkan rubuce-rubucen Shehu Usman Dan Fodiyo, cewa ba inda ya nuna kada a ci naman akuya ya yi tasiri,” inji shi.
Bello Abdullahi Tangaza Bafullatani ne, ya ce tosorn ciwon kuturta na daga cikin dalilin da ke sa wadansu mutane kin cin naman akuya da bakin kifi.
Sadiya Attahiru Jabo ta ce su a gidansu gaba daya ba su cin naman akuya da bakin kifi. Haka suka taso gidansu kowa ba ya ci. Ta ce da zarar sun ci shi ko ba su san shi ne ba, dan lokaci kadan kuraje za su fito musu a ko’ina jiki. Don haka ba su cin naman. Ta kara da cewa ita ba ta taba cin naman ba a duk tsawon rayuwarta.
“Ba na ganin ba mu cin sa ne don Shehu ba ya ci, sai don kare lafiyarmu, domin a bayanin da na samu; ba naman da Shehu Dan Fodiyo ke so kamar naman akuya da nononta. Ya bar cin naman ne kan alwashin da ya yi wa Ubangiji Allah, dagane da wani yaki da ya fita, ya ce in ya samu nasara zai bar cin abin da ya fi so a rayuwarsa. Hakan ya sa ya bar cin naman akuya,” kamar yadda ta yi karin bayani.
Rabi’atu Muhammad Bello, a zantawarta da Aminiya ta ce ita Bahaushiya ce amma ba su cin naman akuya kan wani dalili da ya shafi gidansu. Ta ce bayan ta girma ana aikenta yin cefane a gidansu, mahaifiyarta takan gargade ta, cewa duk lokacin da aka aika ta sayen nama, kada ta sayo na akuya.
“Ni a zatona ba komai a naman, wata rana na tafi yin cefane na ga naman akuya, na sayo kawai. Da aka dafa shi gidanmu, mahaifiyata ta ci. Nan take ta rikice mana, sai ga kuraje a jikinta kuma duk jikin nata ya rika rawa. Haka muka tafi asibiti aka ba ta magani kuma ta gano cewa naman akuya ta ci. Daga nan ban kara sayo shi ba kuma ni ban ci ba. Shi kadai ne naman da ba na ci a rayuwata,” inji Rabi.
Umar Bandi Kofar Kware mai shekara 60, ya ce shi yana cin naman akuya. A shekarun baya duk lokacin da ya ci naman sai kuraje sun fito masa amma ya ki dainawa har ya kai yanzu ko ya ci ba abin da ke samunsa.
“A Sakkwato za ka samu masu shekara 60 ne zuwa sama da ke kyamar naman akuya, don gudun kada ciwon zafi mai sanya kuturta ya same su, amma masu shekara 30 zuwa kasa ba ruwansu suna ci kuma ba ya yi musu komai don sun dauka nama ne kamar sauran naman ni’ima,” inji Malam Umar.
Alhaji Abubakar Mainama da ke Unguwar Sabaru yana sana’ar fawar akuya. Ya ce kafin samun wannan karayar tattalin arziki da ake ciki suna yanka akuya 100 a rana, inda cikin masu sayen naman akwai Fulani da Yarbawa da Ibo.
“In naman yana da matsala gare su can baya ne, yanzu bai yi musu komai. Ko’ina mutane suna sayen naman. Kafin wannan yanayi, muna yanka akuya 100 amma yanzu sai mu yanka biyar don mutane ba su da kudi,” kamar yadda ya yi bayani.