✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin da Obasanjo ya sa aka kama ni –Sarkin Sasa

Mai martaba Sarkin Sasa Sardaunan Yamma kuma shugaban Majalisar Sarakunan Hausawa na Jihohin Kudu, Alhaji Haruna Maiyasin Katsina mutum ne da ba ya bukatar gabatarwa,…

Alhaji Haruna Maiyasin Sarkin Sasa yana bayanin yadda Obasanjo ya sa aka kama shiMai martaba Sarkin Sasa Sardaunan Yamma kuma shugaban Majalisar Sarakunan Hausawa na Jihohin Kudu, Alhaji Haruna Maiyasin Katsina mutum ne da ba ya bukatar gabatarwa, sakamakon yadda sunansa ya yi amo a kasar nan musamman zamanin mulkin marigayi Janar Sani Abacha. Malami ne, basarake ne, kuma shugaban jama’a da yake gwagwarmaya domin kare al’ummar Hausawa ko ’yan Arewa mazauna Kudancin kasar nan. Sai dai a baya-bayan nan ba a jin duriyarsa, lamarin da ya sa jama’a ke tunanin ko yanzu ba a yi da shi ne. Aminiya ta tattauna da shi kan haka da gwagwarmayar da ya sha da kuma dangantakarsa da manyan kasar nan:

Aminiya: Yallabai za mu so mu ji takaitaccen tarihinka da kuma lokacin da ka zo Kudu, kuma shin malanta ce ta kawo ka ko kasuwanci?
Sarkin Sasa: A takaice an haife ni a Katsina sama da shekara 76 da suka gabata, mahaifina shi ne Ardo Malam Muhammadu da ake yi wa lakabi da Gobe-Da-Nisa, wani fitaccen malamin addinin Musulunci kuma shugaban jama’a a zamaninsa. Na yi karatun addini a Gashuwa da Nguru da Maiduguri, kuma na fara malanta ne a Maiduguri.
Aminiya: Ana ce maka Alhaji Haruna Maiyasin Katsina, Katsina daga wace karamar hukuma?
Sarkin Sasa: Asalinmu daga karamar Hukumar Batsari ta Jihar Kastina ne, wanda ya haifi mahaifina dan Katsina ne, wadda ta haifi mahaifiyata ’yar Katsina ce, tattaba-kunnen danwaire ce. Ni Basullube ne, mahaifina Bafillace ne.
Aminiya:  Yaya aka yi ka samu lakabin Maiyasin?
Sarkin Sasa: Sunan da ake yi wa mahaifina lakabi ne, wato Maiyasin.
Aminiya: Wato ka gaji malantar ke nan, to a ’ya’yanka akwai wanda kake ganin zai gaje ka?
Sarkin Sasa: kwarai kuwa akwai su.
Aminiya: Shin kasuwanci ya kawo ka Kudu ko malantta?
Sarkin Sasa: Sha’anin malanta ya kawo ni Kudu. Gwamnatin Tarayya ta kawo ni a zamanin mulkin Janar Yakubu Gowon. Yakubu Gowon da Janar Shehu Musa ’Yar’aduwa suka kawo ni nan sama da shekara 40. Allah Ya yi zamana a nan ina almajirci. A haka na kasance tare da gwamnati har Allah Ya nufa cudanyar da nake yi da jama’a da irin gwagwarmayar da nake yi, suka yarda da ni na jagorance su, kuma ganin haka ya sa Olubadan na Ibadan Alayeluwa Oba Yusuff Oloyede Asanike ya ba ni sarautar Sarkin Sasa a 1984. Da farko na ki yarda, na ce ba na so. Daga nan kuma aka ba ni Otun Giwa Addini na Jihar Oyo a 1989. Yanzu ina tsammanin ina da sarauta 15, kuma an karrama ni da digirin dokta guda 21. Ba zuwa nake yi ina roko ba, a’a ana ba ni ne. Daga baya sarakunan Hausawa na jihohin Yamma da Kudancin kasar nan suka taru suka ce suna so zu zabe ni shugabansu, na ce ban yarda ba. To, lokacin da aka ba ni digirin dokta suka zo nan suka ce, maganar da muke gaya maka cewa za mu ba ka shugaba na sarakunan Hausawa ce ta sake kawo mu. Na ce me ya sa ba za ku tambaye ni dalilin da na ki ba. Sarkin Hausawan Oyo da Sarki Kabiru na Legas suka tambaye ni. Na ce, abin da ya sa na lura ba zaman gaskiya ake yi ba, in kun yarda mutumin da duk ya yi laifi koda Sarki ne ko dan Sarki ne, in ya yi laifi a hukunta shi, to na yarda, suka ce sun yarda. To ka ji dalilin sarautata ke nan.To, Allah da ikonSa na tafi Abuja, lokacin da aka ba ni Garkuwan Gamji na daya wanda Sakataren Gwamnatin Tarayya Alhaji Gidado Idris ya mika min takarda, sai suka hadu suka zo nan gidan cewa sun zo su nada ni sarautar da ban so. Na ce kun ji abin da na gaya muku, sai na yi waya ga yarana a gida cewa a kama shanu biyu a yanka a yi abinci ga baki, ina can Abuja suka ba ni sarautar, ba ina gida ba.
Aminiya: A ganinka me ya sa sarakunan Hausawa suka mika maka wuya ka jagorance su?
Sarkin Sasa: Wannan Allah ne Ya kaddara, ba dabarata ba ce. Allah ne Ya sa suka zabe ni in jagorance su. Su suka san dalilin da ya suka ce in jagorance su.
Aminiya: An kira ka Sardaunan Yamma, me ya sa aka kira ka da Sardauna?
Sarkin Sasa: kila cancanta, ka san duk dan Arewa na kirki yana son ya kwaikwayi aikin Sardauna. Wasu dabi’u da Sardauna ke da su, su ne sadaukar da kai ga jama’arsa da kuma kyauta, to, ba yabon kai ba, ina kokari don kare jama’ar Arewa mazauna Kudu, kuma ina koyi da shi wajen kyauta, misali in na samu Naira miliyan daya a yanzu haka, ga jama’a zan rabe ta, in ba wasu sun kama sun shigar da wasu cikin gidana ba. Na yi kyautar da ban san adadinta ba, zai yi wuya in ga mutum yana jin yunwa a ce ban ba shi ba. Lokacin da nake da hali, na yi kyautar mota ta kai 337 a kasar nan. Saboda ban mayar da duniya bakin komai ba. Babu abin da ya kai shuka alheri kyau, idan kana da abinci makwabcinka ba ya da shi, sai ka dora tukunya ya ji kanshi ka bar shi da yunwa kana da alhakin makwabcin a wuyanka.  
Aminiya: Baya ga Hausawa da ’yan Arewa  wasu kabilu da mutanen Nijar da Ghana da Togo da Benin da sauransu suna zuwa neman taimakonka, ko gwargwamayarka wajen nemo musu hakki ne ke jawo haka?
Sarkin Sasa: Muna tare da kowa, in ka zo nan gidan ba mutanen da ba za ka gani ba. In ka ga ina rigima da mutane, watakila macuta ne, masu cutar al’umma.
Aminiya: Da Shehu ’Yar’aduwa da Yakubu Gowon suka kawo ka akwai shawarwarin da kake ba su ne ko kuma malanta kawai kake yi?
Sarkin Sasa: Sun kawo ni a matsayin malaminsu ne. Lokacin da na zo, sun ba ni mota, soja ke tuka ni, soja ke raka ni duk inda zan je. Lokacin da mulkin soja ya kau, Shagari ya kama, sai aka tasar min da rigima iri-iri, amma Allah Ya kare ni.
Aminiya: Me ya sa suka zabi ajiye ka a nan Ibadan maimakon Legas fadar gwamnati?
Sarkin Sasa: Da farko an ajiye ni a Legas, to amma saboda irin bincike-bincikenmu na almajirai, sai na ce ba na son Legas. Sai aka kawo ni nan Ibadan gidan wani wanda ya yi Minista lokacin Sardauna ana kiransa Oloku aka sauke ni. Na zauna gidansa, su Akinloye da Akinjide su ne manya a lokacin a Yarabawa.
Aminiya: Ga shi kai Bahaushe ne ka zo tsakiyar Yarabawa, yaya dangantaka ta rika gudana da shugabannin Yarabawan kasancewar kana kusa da gwamnati?
Sarkin Sasa: Dangantarmu tana da kyau, ban yarda kusancina da gwamnati ya bata tsakaninmu ba, shi ya sa suka ba ni sarautu.
Aminiya: Akwai manyan Yarabawa da suka yi fice kamar su Awolowo da Abiola da Aresokola da sauransu, a yayin zamanka da su akwai wata ma’amala da ka yi da su?
Sarkin Sasa: Duk muna ma‘amala da su kwarai da gaske, babu wani babba a nan kasar Yarabawa wanda ba na hulda da shi.
Aminiya: A huldarka da su me ya fi burge ka, ko kuma akwai wani abin da suka yi da za ka iya cewa ba su kyauta maka ba?
Sarkin Sasa: Babu wani abu da suka yi min wanda zan ce ba su kyauta min ba, muna huldar kirki da su. Ban ga wata matsala tsakanina da su ba, muna zaune lafiya, ban ga inda suka cutar da wasu ba, kuma babu inda suka cutar da mutanenmu, ana zaune lafiya da su, sai dai sabani wanda ba a rasa ba.
Aminiya: Da mulkin soja ya dawo lokacin Janar Buhari ya tuntube ka ko bai yi ba?
Sarkin Sasa: Ya tuntube ni, saboda babu wanda ban yi hulda da shi ba, da wanda yake mulki da wanda ya yi ya sauka ina tare da su, sun san ni na sansu.
Aminiya: A lokacin mulkin Janar Abacha ne duniya ta fi jin amonka, me ya sa aka fi jinka a zamaninsa, ko shi ya fi karfafa hulda da kai?
Sarkin Sasa: Kafin Janar Abacha ya zo, ina da daukakar da Allah Ya yi mini. daukaka da sanin da jama’a ta yi min, suka sa Janar Abacha ya san ni. Duk da na san Abacha tun yana karamin hafsa mai anini daya (2nd Lieutenant) lokacin ina tare da su. Kuma abin da ya sa muka fi shakuwa da Abacha shi ne, Abacha mutum ne mai jin shawara. Yana jin maganata kwarai da gaske, kuma yana jin maganar malamai da manyan mutane, ana ba shi shawara yana saurare, shi ya sa ya bambanta da wasu masu mulki, shi da Janar Babangida. Saboda wasu masu mulkin, ba su daukar shawara daga masu ba su shawara tagari, kyamarsu suke yi. In dai gaskiya kake fada musu ba za su saurare ta ba.
Aminiya: Abacha ya zo a lokacin da ake rikicin siyasa, saboda soke zaben 12 ga Yuni, kasar Yarabawa ta yi dumi, kai kuma ga shi kana tsakiyarsu. Wace irin rayuwa ka yi a wannan lokaci?
Sarkin Sasa: kwarai da gaske haka ne, amma duk da haka abin da nake yi ban fasa ba, saboda ban razana ba. Ka san shugaba matsoraci ba zai kare al’ummarsa ba, Allah bai hada ni da tsoro irin wannan ba. Ina tare da Abacha duk da wannan rudu da ya faru, ina tare da su ina cikinsu. Na ce maka Abacha mai jin shawara ne, sai ya ce wannan June 12, yaya za mu yi da shi? Na ce ya turo min Janar Gumel ya ba da kudin sadaka za mu yi jana’izar rigimar. Ya turo Janar Gumel ya zo ka san almajirai suna da ’yar dabararsu da Allah Ya yarda da ita. Shi ke nan muka yi rokon Allah aka yi jana’izarta. Na ce masa mun yi jana’izar June 12, ba za ta kara tasiri ba, sai dai a rika jin alamarta, kuma tun sannan ba ta kuma tasiri ba.

Aminiya: Da siyasa ta yi zafi kai kanka kana cikin wadanda kungiyoyin Yarabawa masu goyon bayan Cif MKO Abiola suke jin haushi, inda har aka yi yunkurin kai maka hari a wancan lokaci, yaya kuka yi da su?
Sarkin Sasa: kwarai da gaske an kawo harin, amma Alah bai yarda ba. Wasu mutane masu neman gwamnatin a nan suna jin haushin ina tare da Arewa, kuma na taba ba wasu daga cikinsu bayanin cewa yaya za a yi su raba ni da Arewa bayan ni dan Arewa ne. Wasu suka zo wurina bare ’yan Arewa?
Aminiya: Bayan Abacha, Abdulsalam ya yi mulki na shekara daya, Obasanjo ya zo ya yi takwas, yaya dangantakarka ta kasance da su?
Sarkin Sasa: Obasanjo ya sha zuwa nan gidan shi da matarsa, amma da ya hau mulki ya so ya halaka ni, saboda wai ina tare da Abacha, Allah ne bai ba shi nasara ba. Da ya hau sai ya ba ni baya, saboda tarayyata da Abacha. Lokacin da Obasanjo ya hau gwamnati na je gidansa ya yi min maganar da ban koma ba, domin ya ce min zai yi aiki a kan Abacha, in ba shi sirrin Abacha. Na ce sirrina tsakanina da Abacha kamar tsakanina da kai ne. Domin Abacha mulki ya yi, kai ma mulki kake yi. Shawara nake ba shi, kai ma shawara kake nema. Da na ji ya matsa yana son sirrin Abacha, sai na ce sirrina da Abacha, shi ne ya ce mu roki Allah kada kasa ta rushe, sirrina da shi ke nan. To, daga wannan lokaci ban sake zuwa wurinsa ba, shi ne sai ya turo min ’yan sanda 12 dukkansu ba Musulmi, sai mutum daya wani Bayarabe. Shi ke nan aka kai ni sel aka yi min tambayoyi aka ce ka san Lateef (Shopolohan) na ce, ban san shi ba. Suka yi ta tuhuma ta suka fahimci zargin ba gaskiya ba ne suka bar ni na dawo gida.
A lokacin Kwamishinan ’Yan sanda ya ce, wai an ba ni kudi Naira dubu 300, na ce ranka ya dade ni fa almajiri ne, idan ana so a kashe mutum sai an ba ni kudi na yi magana da wani mutum. Sai ya ce ina da sirri da Abacha, na ce ina da sirri da Abacha zan gaya maka? Na ce ba zan gaya maka ba. Sai ya ci gaba da tambayoyi cewa na bata dukiyar gwamnati na ba da motoci 100. Na ce karya ne ban ba da mota 100 ba, wanda ya gaya maka na ba da mota 100 karya yake maka. Na ce shekara kaza ni mai hidima ga jama’a ne, kuma jama’ar suna yi min hidima. Na ce mota 337 na ba da, ba mota 100. Ya ce daga cikin kudin gwamnati ne na ba da, na ce a’a, ina zan samu kudin gwamnati ni ba ma’aikaci ba. Ni almajiri ne idan zan yi kyautar mota dubu ina ruwanku?
Na sha rigingimu da su, Obasanjo ya nemi hanyar da zai halaka ni, Allah bai nufa ba, saboda ina tare da Abacha. Ina tare da Abacha, shi Abacha ba ya tarar da ni ina tare da wasu ba? Ai ya tarar da ni tare da wasu, shi ya ki ni ne, saboda ina tare da wasu? To yaya su za su ce saboda ina tare da Abacha ba su tare da ni? Wannan ai jahilci ne, tunda Abacha ya riga ya rasu. A lokacin duk wanda yake tare da Abacha an ji masa, in kai soja ne, sai a raba ka da aikinka, ko a kai ka wurin banza ko a kore ka, haka kawai don kana tare da Abacha.
Aminiya: Ko akwai wani abu da ka yi wa Abacha ne ya sa mutane suke ganin ya fifita a kan sauran malamai?
Sarkin Sasa: Tsakaninmu da Abacha soyayya, kuma yana karbar shawara, yana jin maganar wadanda suke gaya masa gaskiya. Ina tare da shi ne saboda Allah, duk abin da na ga zai kawo cikas nakan ce kada ya yi, kuma ba zai yi ba.
Aminiya: Umaru Musa ’Yar’aduwa kanen Shehu ’Yar’aduwa ne wanda ka ce shi ya kawo ka nan, ya yi mulki, ko ya ci gaba da harka da kai?
Sarkin Sasa: Muna tare da su, ni dan gida ne a wurinsu. Shi Umaru ’Yar’aduwa bayan ya rike gaskiya da malamai bai ga bayan ’yan Neja-Delta ba, wadanda suka dauki makamai ba?
Aminiya: Bayan Umaru ya rasu wannan gwamnati ta Jonathan ta shigo, akwai wasu daga cikin mukarrabanta da suke tuntubarka don a yi musu rokon Allah?  
Sarkin Sasa: Suna zuwa amma ba da yawa ba. Kuma rashin rike malamai ne yake kawo tabarbarewar al’amura a kasar nan.
Aminiya: To, yanzu za a iya cewa ba ka tare da gwamnati ke nan?
Sarkin Sasa: Ina tare da gwamnati, amma ba su yi da ni. Saboda babu wanda yake zuwa ya ce, Malam a roka mana Allah a samu zaman lafiya in ban da Gwamnan Jihar Gombe (Alhaji Ibrahim dankwambo), shi kadai yake turo sadaka, ya ce a ci gaba da addu’a Najeriya ta zauna lafiya.
Amma in ba haka ba, babu wani Gwamna ko Minista ko Sanata da ke aiko sadaka gidan nan koda na abinci, sai dai Gwamnan Jihar Gombe kawai, shi yake aiko sadaka yana cewa kada almajirai su bar gidana a ci gaba da rokon Allah neman zaman lafiya a Najeriya, wadannan rigingimu Allah Ya kwantar da su.
Aminiya: Galibi lokacin mulkin siyasa an fi samun tashin hankali, ga shi ka ce shugabannin siyasa ba su cika tuntubar malamai ba, alhali sojoji da suke da bakin bindiga suna tuntubarsu, hakan bai nuna sojoji sun fi son a zauna lafiya?
Sarkin Sasa: Babu mai son fitina, sai in Allah Ya kawo ta, sojoji masu tsaro ne, su kuwa ’yan siyasa masu mulki ne. Rigingimun ma ai siyasa ta kawo su, in ba siyasa ba, ina yaro zai shiga cikin rediyo yana zagin sarauta. da ya shiga talabijin ya zagi mahaifinsa, kane ya shiga rediyo ya zagi wansa?
Aminiya: Kai dan Arewa ne mazaunin Kudu, ka ga irin abubuwan da suke faruwa a Kudu da wadanda suke faruwa a Arewa. Yaya za ka kwatanta shugabannin Arewa da na Kudu?
Sarkin Sasa: To, ka san su shugabannin Kudu suna da hadin kai. Yanzu in mutum yana da kudi a Kudu, yana iya daukar ’ya’yan talakawa ya biya musu kudin makaranta. Yana iya kafa kamfanonin da mutanensa za su samu aikin yi, amma Arewa ba a yi. Kuma nan Kudu masu goyon bayan al’ummarsu ne, mu kuwa ba ma goyon bayan al’ummarmu.
Aminiya: Da ka tabo batun goyon baya daga bangaren talakawa ne ko shugabannin?
Sarkin Sasa: Daga bangaren shugabannin ne, abin da aka nuna wa talakawa ba shi za su yi ba? Kana hulda da bangarorin jama’a da yawa ka nuna ba ka son wani, da haka za a so shi?
Aminiya: Rikice-rikicen da suke faruwa a Arewa mene ne mafita?
Sarkin Sasa: Mafita a tsaya ga Allah, shugabanni su tsaya kan gaskiya, su yi adalci, in an yi haka al’amura za su gyaru. Rashin adalci ke kawo matsalolin kasar nan, kuma a taimaka wa bayin Allah. A kawar da rashin aikin yi, saboda mutum ya tashi da safe babu abin yi shi zai kawo rigima, don in wani ya jawo shi zo ka yi barna zai je ya yi. ’Yan siyasa ne suka bata kasar nan, tunda su suke ba yara kayan shaye-shaye su ce ku zo ku bi mu, su ba su adduna da sanduna da sauransu su ce ku zo ku bi mu, in lamarin ya bukansa a hada da bindigogi. Kuma in aka ci zabe aka kwana biyu sai su yi watsi da su ba za su kula da su ba. In da mutumin da aka taimake shi ya hau mulki yana kulawa da na baya, wadanda suka taimake su yana dan sama musu ayyukan yi ba za a yi fitina ba.
Aminiya: A baya lokacin Turawan mulkin mallaka na amfani da sarakuna wajen mulkin jama’a, yanzu sai aka janye hannun sarakuna daga mulki, me za ka ce?
Sarkin Sasa: Raba sarakuna da mulki shi ya tabarbara al’amura a kasar nan. Sarakuna su ne suka san jama’a, aka ce ba a yi da su, sai mutum ya zama kansila daga nan ya zama ciyaman, sai ya zo ya ce sarki kaza bai dace ba a cire shi, sai ya sa a dauki shakiyyi a nada. Sarakunan nan da aka maida kamar motar kwana-kwana, sai wuta ta kama a neme su, shi ne tushen lalacewar al’amura. Sarki shi ne shugaban jama’a, abin da sarakuna suka sani gwamnati ta sani ne?
Aminiya: In aka ce ka ba da shawara ga ’yan baya game da yadda rayuwa take me za ka ce musu?
Sarkin Sasa: Abin da zan ce, duk abin da mutum yake yi ya rike Allah, ya tsaya kan gaskiya. Domin idan Allah Yana son mutum sai Ya ba shi kunya, Ya ba shi gaskiya da hakuri, ya tafiyar da ayyukansa bisa daidai, ya je Lahira ya shiga Aljanna. Idan kuma Allah bai son mutum, sai Ya ba shi rashin kunya, Ya ba shi rashin hakuri, Ya ba shi girman kai, ko an gaya masa gaskiya ba zai ji ba.
Yadda za a gyara al’amura shi ne a koma ga Allah, a ci gaba da rokon Allah. A ci gaba da zumunci da adalci, sai ka ga Allah Ya raba mu da wadannan rigingimu. Amma in aka ce ba za a koma ga Allah ba, abubuwa za su ci gaba da lalacewa. Ka duba a Najeriya ne ake sassare mutane ana fawarsu kamar shanu, a tsare mutum a sassare shi a kashe saboda kudi, a ce za a zauna lafiya. da ya taho yana zagin mahaifinsa babu mai ce masa ya bari.
Aminiya: Wane kira za ka yi ga Hausawa mazauna Kudu?
Sarkin Sasa: Kiran da zan yi ga Hausawa mazauna Kudu, sun rike addininsu, su rike Allah su riki gaskiya. Kuma su rika hakuri kamar yadda aka san mutanen Arewa da shi, a rika jan mutane a jiki a bar kyamarsu. Abin da ke kawo rigima mutum ya ji warin wani ya ce wari yake yi, ba za a zauna lafiya ba.