Aminiya ta zanta da masanin tattalin arziki, Ambasada Abubakar Ali inda ya yi bayani a kan dalilin da Najeriya ba za ta rika buga kudi maimakon ciyo bashi ba. Kuma ya tabo dalilin yawan karyewar darajar Naira da gajiyar da yake samawa a kasashe masu karfin tattalin arziki:
Ko kasa za ta iya buga kudi mai yawa don biyan bukatun kanta maimakon cin bashi kamar yadda wadansu ke tsokaci?
- Barayin waya a kan Adaidaita Sahu sun hallaka matashi a Kano
- Shekara 10 da kisan Ghaddafi : Gara jiya da yau a kasar Libya?
Lallai nakan ji wadansu suna irin wannan magana, sai dai abin da ya kamata su sani shi ne, shi kudin kasa ba takardar banza ba ce, da za a buga ta haka nan tamkar takardar gayyatar aure ko makamancinta.
Adadin yawan kudi da kasa za ta iya bugawa yana da dangataka ne da girman tattalin arzikinta ta fuskoki da dama; kamar matakin habakar da take samu da adadin kudin waje da suke shigowa kasar da kuma na ajiyarta da ke waje don bukatun sayayya na ketare.
Dole ne a yi la’akari da ire-iren wadannan matakai ba wai na bukatar kashin kai kawai ba. Yin watsi da wadannan tanade-tanade tare da yin gaba-gadi wajen buga adadin kudi fiye da kimar tattalin arziki, na iya kaiwa ga kudin kasar ya rasa darajarsa tun a cikin gida.
Misali, ko da irin sayayya na yau da kullum kamar na cefanen gida da ake yi a kasuwa, na iya kaiwa sai an yi dakon kudi mai yawa a cikin jaka ko baro kafin a iya yin sa, kamar yadda ya faru a kasar Jamus bayan Yakin Duniya na Farko ko kuma nan kusa a kasar Zimbabwe.
Wani abu da zai sa a buga kudi shi ne idan aka yi la’akari da karancin nau’in kudi a wuraren kasuwanci kamar yadda ake fuskanta a yanzu a bangaren kananan kudi kamar Naira 200 da Naira 100 da Naira 50 zuwa Naira 20. Wannan duk yana faruwa ne sakamakon kudin da suke fitowa daga banki, kamar ATM ko POS duk yawanci manyan kudi ne wato Naira 1000 da Naira 500. To Babban Banki zai iya buga kananan kudi don saukake wa al’umma yin canjin kudi cikin sauki.
Karancin nau’o’in wadannan kudade shi kansa na iya tallafawa wajen rage kimar Naira. Misali idan ana son kara kudin abu a maimakon a yi karin Naira 10 ko 20 ko 50, sai a yi karin sama da haka saboda karancinsu.
Sannan ba daidai ba ne a rika raba wa mutane kudi haka nan, maimakon inganta musu hanyoyi da za su nemi kudin da kansu. Hakan na iya kaiwa ga adadin kudin da suke hannun jama’a ya zarce aikin yi ko na samar da abubuwan bukata da ake da su.
Misali a ce ga kudi a hannun kowa alhali ana karancin abin yi ko samar da na sayarwa, to, sai a rasa wadanda za su yi aikin tunda kowa mai kudi ne. A nan ka ga sai darajar kudi ta yi ta yin kasa. Za dai a iya taimaka wa wadanda dama ba aikin suke yi ba, ta wasu fuskoki.
Kamar ’yan makaranta a tallafa musu ta fuskar ciyarwa da kayan makaranta ko littattafan karatu. Haka kamar ’yan kurkuku a taimaka musu ta wajen ciyar da su, sai kuma gajiyayyu kamar tsofaffi da makamantasu. Amma baya ga wannan fuska sai dai a taimaka wa matasa da sauran masu karfi a jika ta bangaren sana’o’i ko kasuwanci da kuma sama musu wuraren ayyukan yi.
Wane tasiri kudin kasashe masu karfi ke yi ga ire-iren kasashen?
Yana taimaka musu wajen habaka tattalin arzikinsu saboda kayan da masana’antunsu suke samarwa ana sayen su ne kai-tsaye da kudin kasarsu.
Sannan ana ajiyar kudade a kasashen saboda ba a fargabar cewa kudinsu zai karye da zai kai ga yin asara. Haka a daya bangaren darajar kudinsu na taimaka musu wajen rashin ganin tsadar ragowar abubuwa da suke bukata daga wasu kasashe.
Dole ne kasashe irin namu su tashi tsaye wajen sama wa kansu abubuwan da suke bukata maimakon dogaro da na waje.
Hakan shi yake kara raunata darajar kudinmu tare da karfafafa na waje da muke bukata don yin sayayya. Har ta kai cewa ana biyan wadansu ma’aikata da suke aiki a cikin kasar nan da takardun kudin waje maimakon kudin da kasar ta amince da shi.
Hakan ke sa karin bukatar Dalar Amurka kuma ba tare da gwamnati ta hana yin haka ba. Wadansu kuma har wasa da kudin suke yi a wuraren biki wanda hakan ya saba wa dokar kasa. Za ka samu yawanci masu yin hakan wadanda suke da nasaba da gwamnati ne ko iyalansu.
Zai yi wuya ka ga iyalan ’yan kasuwa irin su Alhaji Aliko Dangote ko Alhaji Abdussamad Isiyaka Rabi’u ko Cif Otedola suna yin haka, saboda su sun san dararjar kudin, ba a banza suka same su ba.
Kasashen Afirka sun sha yunkurin samar da kudin bai-daya ba tare da nasara ba. Me kake ji ya jawo haka?
Lamarin bai rasa nasaba da tsayawar kasashe irinsu Faransa da ke da tasiri a kan wasu kasashenmu na Afirka ba. Misali wadanda suke kewaye da Najeriya, har yanzu duk da sun samu ’yancin kansu, amma Faransa ce ke buga musu kudin da suke amfani da su.
Sannan wasu masana’antu da suke cikIn kasashen, ita Faransar ce ke da su, suna jin maganarta sosai. Dole ne kasashenmu na Afirka su hada kansu su sama wa kansu mafita, idan ba haka ba tamkar wani sabon mulkin mallaka ne na zamani suke yi mana ta fuskar tattalin arziki, bayan sun yi mana na bautarwa a baya.
Dole ne mu sauya tsarin kasafin kudinmu wanda shekara da shekaru ya kare a kan abu daya, wato samar da abubuwa irin su titi da lantarki da ruwa, har yanzu mun kasa wuce wajen.
Wannan hannun riga ne da na kasashe da suka ci gaba da ake tafiyar da shi wajen gudanar da bincike da bunkasa bangarorin kimiyya da sauransu. Sannan sai a yi ta aiwatar da abu guda ana handame kudin baya ga yawan kudi da ake ninka masa don arzuta masu nasaba da kasafin.