✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin da na kafa masana’antar kwalliya da shafe-shafe a Amurka – Khuraira Musa

Hajiya Khuraira Musa, ’yar Najeriya ce da ke zaune a Amurka tun 1992, tana da Kamfanin Kwalliya da Shafe-Shafe na Mata a birnin New Jersey…

Hajiya Khuraira Musa, ’yar Najeriya ce da ke zaune a Amurka tun 1992, tana da Kamfanin Kwalliya da Shafe-Shafe na Mata a birnin New Jersey na Amurka. A tattaunawarta da Aminiya, a yayin wata ziyara a Najeriya, ta ce ita ba ta da buri a duniya da ya wuce ta share wa marasa galihu hawaye tare da ganin yankin Arewa ya koma yadda aka san shi a baya ta wajen bunkasar tattalin arziki.

Tarihina:

Sunana Huraira Musa. An haife a Kaduna, na girma a Jos, sa’annan na wuce Amurka karatu; kuma ina zaune a can tare da mijina da ’ya’yana. Na fara zama a Amurka ce a 1992.

Ilimi:

Na yi makarantar firamare, da sakandare inda na yi rubuta jarrabawar GCE da WAEC. Na yi jarrabawar JAMB, daga nan na wuce Jami’ar Ahmadu Bello (ABU), a Samaru. Daga baya na wuce Amurka karatu, na karanta kasuwanci. To daga nan kuma sai na koma harkar sana’ar ‘Kwalliya da Shafe-Shafe’. Na fara harkar kwalliya tun ina karatun jami’a a Amurka, ina yi wa mutane kwalliya. Bayan shekara uku, sai na ga cewar tunani ya fi karkata a harkar kwalliya, sai na yi tunanin ci gaba da harkar. Da na gama karatun jami’ar sai kawai na fara yin sana’ar a duk jihohin Amurka ina koya wa wadansu masu sana’ar yadda za su yi.  Sannan sai likkafata ta yi gaba, inda na zama mai horarwa a kan kwalliya ta kasa da kasa. Na yi  a Kanada da Ingila da kuma Amurka din.

Burina ina karama:

Ni burina ina karama, bai wuce kawai in sayar da nono, wato iya nan burina ya tsaya. In dan tara kudina, saboda a ruga aka haife ni, na girma a ruga. Sai da na yi aure na shiga cikin gari. Da na yi aure a Kaduna, sai na fara tunanin ni fa zan so in zama mace mai kasuwanci, kuma burina Allah Ya rufa min asiri in samu kudi in koma kauyena in taimaka wa mutane, saboda na taso cikin talauci. Duk burina in samu kudi in taimaka wa mutane. Kuma alhamdulillah, Allah Ya yi min rufin asiri daga aikin kwalliya da nake yi da kuma koya wa mutane da masana’antata take yi a New Jersey.  Muna sayar da kayayyakinmu a duniya baki daya har da nan Najeriya. Daga wannan ribar ce na gina makaranta ta ’ya’yan talakawa Musulmi da Kiristoci.  A shekarar 2013 muka bude ta da yara 22, yanzu muna da yara kimanin 100.  Kuma ni nake biyan malamai albashi da sauran harkar gudarnarwa, daga ribar da na ke samu a masana’antar kwalliyata. Ba a cajar yaran ko kwabo, kyauta suke karatu.

Kalubalen rayuwa:

A shekarar 2013, dan autana, Hanif an haifi shi da sikila, to sai ya samu matsalar huhu, inda dukkan huhunshi suka baci. Ba ya iya numfashi aka saka shi a dakin gobe- da-nisa, an ce ma ba zai iya rayuwa ba, watansa uku yana numfashi da na’ura. Allah dai Ya taimake mu sai muka samu ya farfado, aka zo aka yi masa dashen bargo. Ni na ba shi bargona, aka yi masa dashe. Alhamdulillah yanzu ya warke, shekararsa biyar ke nan yanzu a wannan Satumban da warkewa daga cutar sikila. To a wannan lokacin na fuskanci kalubale sosai, ka ga danka a wannan yanayi a ce ma ba zai iya rayuwa ba. Abin tsoro ne gare mu gaskiya, ba ma ni kawai ba, duk da sauran iyalina. Amma yanzu alhamdulillah komai  ya yi kyau.

 Nasarorina:

Daga makaranta na samu sakamako na kwaloluwa a jarrabawa, (Distinctions), sai harkar kasuwancina na kasance kullum kan gaba, inda da nake wa wasu kamfanoni aiki, kuma ni ce mace baka ta farko da ta taba aikin kwalliya da ake kira ‘Top Brands’ da masu kudi ne kawai ke amfani da shi a Amurka. Ni ce mace bakar fata ta farko da suka fara dauka ina ba da horo ko koya wa mutane irin wannan kwalliya a Amurka da sauran kasashen duniya. Ba daidai ba ne ana maganar launin fata; amma gaskiyar al’amarin ke nan. Kuma da na fara harkar shafe-shafe Kamfanin Oprah ya zabi hodar kamfanina a zaman mafi kyau kuma har yanzu shi ya fi kasuwa. Mujallu da dama sun wallafa kayayyakina a zaman na kan gaba da suka yi zarra cikin tsara. Mujallun su ne Cosmopolitan Magazine da Banity Fair, sai kuma Essence Magazine. Kuma shekara biyu da suka gabata, an zabi kamfanina a zaman na kan gaba ta fuskar kwalliya da shafe-shafe a Jihar New Jersey.

 Musulunci ya saka ni shiga harkar kwalliya da shafe-shafe:

Da na je Amurka, ko’ina na je aiki sai na tarar maza ne kawai; ina so duk inda zan yi aiki ya zama mata ne kawai wajen. Don ba na son shiga ina gwagwarmaya cikin maza, sai na yi tunanin shiga harkar kwalliya da shafe-shafe, wadda mata ne kawai suke yi. Yau da za a koya wa matanmu a nan Najeriya, har abin ya zama na kasuwanci, ko matan kulle (matan aure) ma za su yi. A zo a koya musu, suna yi a cikin gidajensu ana sayarwa su ciyar da kansu su ciyar da iyalansu. Ina tunani da burin in ga ana kera abubuwan kwalliya a Najeriya, ta yadda abin zai yi kima sosai, ba wai ina nufin a kawo Huraira Cosmetics ba ne. Ina da yadda zan yi in koya wa mata su sarrafa albarkatun man kwakwa da na ’ya’yan dalbejiya ta ingntacciyar hanya mu daga darajarsu sama ta fuskar kwalliya har mu sayar da su a Amazon da Wallmat da Jumia, wanda zai kara wa kasar samun kudin waje.

 Abin da nake son a tuna ni da shi:

Ba ni da burin tara abin duniya a rayuwa. Ina so in ga duk abin da na mallaka na share wa wani hawaye da shi. In da zan mutu a ce yau babu ko kwabo a asusuna a banki; bai dame ni ba. Kawai in dai wani zai ce, saboda Huraira na samu kaza, ko na fita daga matsala kaza shi ke nan. Wato yau a ce wani ya tashi ya ce na yi makaranta saboda Huraira; wani ya ce na samu lafiya saboda Huraira, ko na yi kasuwanci saboda Huraira, wannan shi ne abin da nake so a tuna da ni ke nan. Ba wai burina in tara gidaje, in tara motoci ba. Ba abin da ke kaina ba ke nan. Ina burin in na mutu wani ya ce don Huraira na fita daga wannan matsalar ko na samu alfarmar wannan.

Don haka abin da na fi so shi ne yadda zan taimaka wa mutane. Ina rayuwa da wannan kullum. Ina tunanin hanyar  yadda za a  gyara rayuwar mutane, hakan na saka ni farin ciki. Ina son ayyukan taimako.  Ina son lokaci na kashin kaina, kamar ranar Litinin ranata ce wannan, kuma ma ko a wannan ma ina tunanin me zan yi a gaba.

Shawarata ga mata:

Ga mata ya kamata su tashi, idan ana yi miki abu ki fito fili ki fada, in bai miki dadi ba; ba za a kashe su ba; hanyar fahimtar juna ce kawai da ke da maigidanki. Amma ba wai ta hanyar rashin kunya ba. Kuma su saka ’ya’yansu a makaranta. Namiji ba zai iya daukar komai ba. Kamar matan kabilu za su zauna da zani guda, don su kai ’ya’yansu makaranta. Mata ku daina kashe kudi a biki, ya kamata ku kai ’ya’yanku makaranta. Misali ni da aka haife ni a ruga; da Mamata ba ta kai ni makaranta ba, da ba zan yi ilimi har in je Amurka kuma muke tattaunawa da kai ba.

   Hajiya Khuraira Musa tare da iyalinta
Hajiya Khuraira Musa tare da iyalinta

Shawarar mahaifiyata  da ba zan manta da ita ba:

“Kada ki damu da halayen mutane ki damu da abin da ke gabanki, duk yadda kika yi ba za ki canja mutane ba, Huraira.”

“Kada ki rika wulankata mutane, saboda kowa kabarinsa daban. Kuma in Allah Ya rufa miki asiri; ba ki taimaka wa ’yan uwanki ba, to fa ke talaka ce har abada; don haka ki rika taimaka wa ’yan uwanki.’’  Kuma ina kokarin dabbaka hakan.

Mata na iya hada karatu da aure:

Kwarai mata na iya hada karatu da aurek, kamar makarantar da na bude a Karamar Hukumar Bassa a Jihar Filato, wadda na  bude don tunawa da mahaifiyata, Hajiya Zainab Memorial School, yarjejeniyar da muka yi da iyaye da kuma mijin da zai auri yarinya shi ne duk wacce aka yi mata aure a shekara 15 zuwa 16 za ta je zauna a gidanka amma za ta ci gaba da zuwa makaranta sai ta gama sakandare. Kuma muna son mu kirkiro da cibiyar koyar da sana’o’i ta gaba da firamare; don koya wa irin wadannan matan da aka yi wa aure kuma ba za su dawo ba, sai a koya musu sana’o’in hannu don su rika dogaro da kansu. Amma in sun ga suna iya dawowa daga baya, shi ke nan sai su dawo.

Iyalina:

Ina da miji da ’ya’ya biyar; maza hudu mace daya.

Tufafin da na fi so:

Na fi son irin kaftani; wato kayanmu na Hausawa da Fulani.

Hutu:

Idan na samu hutu akasari sai na zo Najeriya, in kuma na zo ina zuwa in ga makarantar da na kafa; sannan sai in ziyarci dangina. Kamar a Amurka da yake akwai ranakun hutu da dama, na fi son hutun ranar cika-ciki da ake yi da iyalai a watan Nuwamba. Sai kuma sauran ranakun hutu. Ina sauraren wakoki dan kwantar  da hankali na, musamman ma idan ba ni da lafiya.

Kasashen da na ziyarta:

Na je Saudiyya, na yi Hajji sau biyu sai kuma Umara sau uku. Na je Jamus, na je Kanada na je Ingila na je Faransa, Amurka kuma can na ke zaune. A Afirka na je kasar Ghana.

 Yadda na hadu da mijina:

Mun hadu da shi a wajen aiki, a birnin  New York.

Abin da na fi so daga mijina:

Yana da matukar hakuri, kuma mutum ne mai saukin kai; kuma uba ne na kwarai. Sa’annan kuma ya iya girka abinci.

Mawakan da na fi so:

Mawakin da na fi so shi ne Nazir M. Ahmad, Sarkin mawaka.

Ina kuma son Celendion, ina son John Legion sai kuma mawakiyar Birtaniyar nan Adele, sai kuma Bryon Nick Night da sauransu.

Abincin da na fi so:

Da na fi son shinkafa. Amma saboda lafiyata, yanzu na fi son ganyanyaki da kuma masu gina jiki.

Kungiyoyin  da nake ciki:

Ina cikin kungiyar masu rajin yadda za a samu bargo a wani asibiti a yankin Westchester a  New York, don taimaka wa marasa karfi  da ke fama da sikila. Sai kuma wayar da kai a kan  ciwon sankarar mama a Amurka saboda abokan cinikina duka mata ne. Sannan ina cikin kungiyar mata 100 Bakaken Fata a Amurka. Sai kuma wata kungiyar da muka kafa a baya-bayan nan a nan Najeriya mai suna ADSI, (Arewa Debelopment Support Initiatibe) da nufin taimaka wa kanmu da kanmu a yankin Arewa. Ba sai mun jira gwamnati ta yi mana komai ba. Na fara tunanin kafa kungiyar tun shekara biyar baya. Na hada karfi da wadansu da na sani don kafawa tare da samar da muhimman ababuwan ci gaba a Arewa, ta hanyar wannan kungiya ta ADSI. Mun kafa wannan kungiyar ce saboda abin da ke faruwa a Arewa yana ci mana rai. Ba ruwanmu da siyasa, ko addini ko kabila ko kuma yankin mutum, kawai in kai dan Arewa ne ka shigo wajen yunkurinmu na dawo da martabar Arewa.  Muna son mu samu mutum dubu daya kawai daga kowace Jihar Arewa, wadanda za su na bayar da taimakon Naira dubu biyu a wata, don tara kudaden aiwatar da ayyukan Kungiyar ADSI.

Gudunmawar da nake bayarwa:

Ina bayar da shawarwari, ina kuma taimakawa wajen samar wa mutane hanyar dogaro da kai. Ina kuma taimaka wa wadanda ba sa iya zuwa makaranta, ina kuma taimaka wa mata, sai makarantar Zainab Memorial school da na kafa. Ina taimaka wa matasa, sai kuma a yanzu da na kafa Kungiyar ADSI.